
HASKEN MUSULUNCI
February 5, 2025 at 06:07 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
06/08/1446. Laraba.
05/02/2025. Laraba.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {165}
_______________
-
900. An karɓo daga Amru ɗan Sha’aibu daga babansa daga kakansa ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu gadon komai ga mai kisan kai, (wato wanda ya kashe ɗan’uwansa, to, baya gadonsa).‛ Nisa’i da Darul ƙuɗini suka ruwaitoshi, ɗan Abdul Bari ya ƙarfafa shi, kuma Nisa’I ya ce hadisi ne Ma’alulli, kuma sawaba shine dakatar da hadisin akan Amru.‛ (Hadisin dwa’ifi ne).‛
-
901. An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗabi Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa: ‚Wanda ya tsare uba, ko ɗa, ko da toshi yana da abinda ya kasance akansa tare asibai.‛ Abu Dawuda da Nisa’i da ɗan Maja suka ruwaito shi, ɗan Madina da ɗan Barri suka inganta shi.‛ (Hadisin Hasanun ne).
-
902. An karɓo daga Abdullah ɗan Umar Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Walicci na mace kamar nanar nasaba ba’a sayarwa, ba’a kyauta.‛ Hakim ya ruwaito shi, daga hanya Shafi’i, daga Muhamadu ɗan Hassan, daga Abi Yusuf ɗan Hibban ya inganta shi.‛ Baihaƙi yayi masa illah.‛
-
903. An karɓo daga Abi ƙilabata daga Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Wanda yafiku sanin hukuncin gado, shi ne Zaidu ɗan Sabitu.‛ Ahmad da Mutum Huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Abi Dawuda.‛ (Hadisin Ingantacce ne)‛.
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.