
HASKEN MUSULUNCI
February 6, 2025 at 06:12 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
07/08/1446. Alhamis.
06/02/2025. Alhamis.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {166}
_______________
-
*BABIN BAYANIN HUKUNCIN WASIYYA DA KUMA YANDA AKE YINTA DA YANDA AKE AIKI DA ITA*.
-
904. An karɓo daga ɗan Umar Allah Ya yarda da su ya ce; haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu wani abu na haƙƙin Musulimi da yake son yin wasiyya cikinsa ya kwana dare biyu, face wasiyya ce wanda aka rubuta daga gare shi‛. Bukhari da Muslum ne suka ruwaito shi‛.
-
905. An karɓo daga Sa’adu ɗan Abi Waƙƙas Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Na ce wa Manzon Allah ﷺ ya Manzon Allah ni mai dubiyane babu mai dagona, face ɗiyata guda data ke gareni, to, na yi sadaka da sulusi biyu na dukiya? Sai ya ce: ‚A’a, (wato biyu cikin uku na dukiya) sai na ce, ‚To, na yi sadaka da sulusinsa (wato ɗaya cikin uku na dukiyarsa), sai ya ce: ‚Sulusi da sulusi da yawa, haƙiƙa kai kabar wa mai gadonka da wadata shine, yafi maka alheri da kabarsu matalauta suna yawo ga mutane‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛.
-
906. An karɓo daga Aishatu Allah Ya yarda da ita ta ce: haƙiƙa wani mutu ya zo ga Annabi ﷺ sai ya ce, ‚Ya Manzon Allah! Haƙiƙa mahaifi yata an karɓi ranta bata yi wasiyya ba, nayi zaton da tayi magana za ta yi wasiyya da sadaka, tana da lada, idan na yi mata sadaka? ‚Sai ya ce: ‚Na’am.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.