HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 6, 2025 at 06:59 PM
*Assalamu Alaikum* - *_29/04/1440,_* _Lahadi._ *_06/01/2019,_* _Lahadi._ - ** - *Wallafar:* Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan. *Fassarar:* Aliyu Muhammad Sadisu *Wanda ya duba:* Attahiru Bala Dukku - *DARASI NA (055)* *__________________* - *_•┈┈┈┈•﷽•┈┈┈┈•_* - _Kore imani dangane da wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukarba._ - _Yana nuna cewa ashe hukunci da shari’ar Allah imanine kuma aƙidace kuma bautawa Allah ne, wannan ya zama kowanne musulmi ya bautawa Allah dashi, ba wai za’a yi hukunci da shari’ar Allah bane don cewa hukunci da ita shi ya fi yi wa mutane kyau kuma shi ya fi tabbatar da tsaro ba._ - _Domin wasu sun fi maida hankali akan wannan ɓangaren, sai su bar ɓangaren farko._ - _Kuma Allah maɗaukakin sarki haƙiƙa ya aibanta waɗanda suke hukunci da shari’ar Allah domin fa’idar kansa ba wai domin bauta ga Allah maɗaukakin sarki ba._ - ```Allah mai girma da ɗaukaka yana cewa:``` - _*(“Kuma idan aka kirayesu izuwa ga Allah da Manzonsa domin ya yi hukunci a tsakaninsu kawai sai wasu tawaga daga cikinsu su juya baya, idan kuwa ya kasance su suke da gaskiya sai su zo wurinsa a guje”)*_. Suratun Nur, aya ta: 48-49. - _Su basa himmatuwa sai akan abinda suke so, abin kuwa da ya saɓawa son zuciyarsu sai su kawar da kawunansu daga gareshi, domin su basa bautawa Allah da kai ƙararrakinsu wurin Manzon Allah (ﷺ)._ - *Allah ka datar damu.* *__________________* _Muhammad bn Umar_ " DAGA Zauren *HASKEN MUSULINCI* " Ga masu buƙatar shiga zauren sai su aiko da cikakkiyar sallama tareda cikakken suna ta wannan number ɗin ta whatsApp sai su faɗi buƙatar su +2348133045868 " Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb " سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك

Comments