
HASKEN MUSULUNCI
February 7, 2025 at 08:03 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
08/08/1446. Juma'a.
07/02/2025. Juma'a.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {167}
_______________
-
907. An karɓo daga Amamatal Bahili Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa: haƙiƙa Allah ya bada dukkan ma’abucin haƙƙi haƙƙinsa, to, babu wasiyya ga mai gado.‛ Ahmad da mutane huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Nisa’i. Ahmad da Tirmizi sun kyautata shi, ɗan Khuzaima da ɗan Jarud suka ƙarfafa shi.‛ (Hadisin ingantacce ne).‛
-
Daga Darul ƙuɗini daga Hadisin ɗan Abbas Allah Ya yarda da su, ya ƙara a cikin karshen sa: ‚Sai dai masu gado, idan sun so.‛ isnadinsa mai kyaune.‛
-
908. An karɓo daga Mu’azu ɗan Jabal Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Annabi ﷺ ya ce: Haƙiƙa Allah yana yin sadaka da sulusin dukiyar ku, a lokacin mutuwar ku, ƙari a cikin kyawawan ayyukanku.‛ Darul ƙuɗini ya ruwaito shi.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne). Ahmad da Bazzari sun ruwaito daga Hadisin Abi Darda’i.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛
-
Kuma ɗan Majah ya ruwaito shi, daga Hadisin Abi Huraira Allah Ya yarda da shi, dukkan ta mai rauni ce, Amma sashe yana ƙarfafa sashe, Allah shine Mafi sani.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛
-
*BABIN BAYANIN HUKUNCIN AJIYA DA YANDA AKE KARƁA.*
-
909. An karɓo daga Amru ɗan Shu’aibu daga babansa daga kakansa Allah Ya yarda da su, daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Wanda aka ba shi wani ajiya, to, (idan ta halaka) babu biya kansa.‛ ɗan Majah ya ruwaito shi, a cikin isnadinsa akwai rauni.‛ (Hadisin Hasanun ne).
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.