HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 8, 2025 at 07:25 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 09/08/1446. Asabar. 08/02/2025. Asabar. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {168} _______________ - *LITTAFIN AURE BABIN BAYANIN HUKUNCIN AURE DA YANDA AKE NEMAN AURE DA KUMA WASU ABUBUWA DA SUKA SHAFI AURE.* - 910. An karɓo Abdullahi ɗan Mas’ud Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Yaku taro samaruka, wanda ya mallaki wurin zama daga cikinku, yayi aure, shine yafi daga rintsewan ido, yafi daga kiyaye wan farji, amma wanda ba shi da ikon, to, yayi azumi, domin shine daab-kansa, daga sha’awa.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 911. An karɓo daga Anas ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ yayi godiya yayi yabo ya ce: ‚Amma ni ina yin sallah, ina yin aure in mace, ina yin azumi ina kuma cin abinci, ina yin auren maccen wanda yayi kyamar, sunna ta baya tare dani.‛ Bukhari da Musulmi suka ruwaito shi.‛ - 912. An karɓo daga gareshi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya kasance yana umurtarmu da wurin zama, yana hanamu kada ita, hani mai tsanani yana cewa: ‚Kuyi auren mai haifan ‘ya’ya masu sayayya domin nayi fariya da yawanku wa Annabawa ranan ƙiyama.‛ Ahmad ya ruwaito ɗan Hibban ya ingantashi.‛ Yana da shaida daga Abin Dawuda da Nisa’i da ɗan Hibban daga Hadisin Ma’aƙil ɗan Yassar.‛ - 913. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Ana auren mace don abubuwa huɗu sune: ‚Domin dukiyar ta, da kuma domin kyawunta, da domin addininta, sai ya rinjaryar da ma’abuciyar addini, ko da hannun ka zai ja ƙasa domin talauci.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, tare masu ruwaya nan bakwai.‛ + 914. An karɓo daga gareshi kuma ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya kasance idan mutum yayi nufin yin aure, sai ya ce: ‚Allah yayi maka Albkarka, Allah ya yi Albarka ya haɗa tsakaninku da Alheri.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi.‛ Tirmizi da ɗan Khuzaima da ɗan Hibban suka inganta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments