HASKEN MUSULUNCI
February 9, 2025 at 06:48 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
10/08/1446. Lahadi.
09/02/2025. Lahadi.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {169}
_______________
-
915. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya sanar damu shaidawa cikin buƙata haƙiƙanin godiya ta tabata ga Allah, kuma muna gode masa muna neman taimakonsa, kuma muna neman gafaransa, kuma muna neman tsarkinsa daga sharrin kawunan mu, kuma dukkan wanda Allah Ya shiryar da shi, to, babu mai batar da shi, kuma dukkan wanda Allah Ya ɓatar da shi, to, babu mai shiryarda dashi, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan Sa ne, kuma Manzon Sa ne, yana karanta ayoyi uku‛.(cewa: ‚Kuji tsoron Allah haƙiƙanin tsoro…‛. Har zuwa ƙarshe ayar. Da kuma ‚Kuji tsoron Allah wanda ake roƙonku da shi…‛ Har zuwa ƙarshe ayan. Da kuma cewa: ‚Ku ji tsoran Allah ku fadi magana mai sauƙI‛ Ahmad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi. Kuma Tirmizi da Hakim ne suka inganta shi‛.
-
916. An karɓo daga Jabir ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Idan ɗayanku zai nemi mace, idan yana da ikon yayi dubi zuwa gare ta zuwa ga abinda aka kirashi zuwa ga aurenta, to, ya aikata hakan‛. Ahmad da Abu Dawud ne suka ruwaito shi‛ Kuma yana da shaida gaga Tirmizi. Kuma Nisa’i daga Mugira‛. Kuma daga ɗan Majah da ɗan Hibban daga Hadisin Muhammadu ɗan Maslimata‛. Kuma daga Muslim daga Abi Huraira ya ce: ‚haƙiƙa Annabi ﷺ ya ce: ‚Wa wani mutum da yayi nufin auren wata ka duba fiskanta? Sai ya ce: ‚A’a, sai ya ce: ‚Ka tafi ka duba fiskanta‛.
-
917. An karɓo daga ɗan Umar Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Kada ɗayanka yayi nema cikin neman ɗan’uwansa har sai mai neman ya bar nema kafinsa ya bari, ko yayi masa izini‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwatio shi‛. Kuma wan nan lafazin ne Bukhari ne‛.
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.