HASKEN MUSULUNCI
February 11, 2025 at 05:31 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
12/08/1446. Talata.
11/02/2025. Talata.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {171}
_______________
-
919. An karɓo daga Amir ɗan Abdullahi ɗan Zubairu daga babansa Allah Ya yarda da su ya ce: haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku ɗaukaka aure.‛ Ahmad ya ruwaito shi, Hakim ya inganta shi.‛ (Hadisin ingantacce ne).‛
-
920. An karɓo daga Abi Burrada ɗan Abi Musa daga babansa Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu aure, sai da waliyyi.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi.‛ ɗan Madini da Tirmizi da ɗan Hibban suka inganta shi, kuma akan illantar da hadisin da cewa Mursal ne).‛ (Hadisin ingantacce ne).‛
Imman Ahamad ya ruwaito shi, daga Hasan daga Imran ɗan Husaini Marfu’an cewa: ‚Babu aure sai da waliyyi da shaidu biyu.‛
-
921. An karɓo daga Aishatu ta ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Kowace macce da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba, auren ta ɓatacce ne, da ta yi idan yayi jima’i da ita tana da sadakin halalta farjinta, idan haka bai samuba, to, shugaba waliyyi ne, idan babu waliyyi: baya da waliyyi.‛ Mutane huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Nisa’I, Abu Awwana da ɗan Hibban da Hakim suka inganta shi.‛ (Hadisin ingantacce ne).‛
-
922. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya ce: ‚Ba’a aurar da marayu, da kuyangi, sai da umurni, ba’a aurar da budurwa, sai an yi mata izini.‛ suka ce: ‚Ya Manzon Allah yaya yin mata izinin yake?‛ Sai ya ce: ‚Idan tayi shiru (bata nuna rashin yarda ba).‛ Bukahari da Muslim suka ruwaito shi.‛
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.