
HASKEN MUSULUNCI
February 14, 2025 at 07:44 PM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
15/08/1446. Juma'a.
14/02/2025. Juma'a.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {174}
_______________
-
934. An karɓo daga Aliyu Alla Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya yi hani game da auren mut’a, a shekarar yaƙin Khaibara‛. Bukhari da Muslim suka ruwaito shi‛.
-
An karɓo daga gare shi, ya ce: ‚Lallai Manzon Allah ﷺ ya hana auren mut’a ( auren jin daɗI, da kuma cin naman jakin gida, a ranar Khaibara‛. Mutum bakwai ne suka ruwaito shi. Sai dai banda Abu Dawud‛.
-
An karɓo daga Rabi’u ɗan Sabra daga babansa Allah Ya yarda da su ya ce: haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Na kasance ina yin muku izini da auren jin daɗi daga mata, to, haƙiƙa Allah ya haramta haka zuwa ranar ƙiyama. Saboda haka wanda ya kasance a wurinsa akwai wani abu daga matan auren mut’a, to, ya wofintar da tafarkinta (ya sake ta) Kuma kada ku riƙI wini abu daga abin da kuka basu, Muslim da Abu Dawuda na Nisa’i da ɗan Majah da Ahmad da ɗan Hibban suka ruwaito shi.‛
-
935. An karɓo daga ɗan Mas’udu Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya la’anci mai auren mace don ya hallata ta ga wanda ya sake ta, saki uku, kuma yala’ancin wanda aka halattawar a gare shi.‛ (Idan yayi umurni a auren).‛ Ahmad da Nia’I da Tirmizi suka inganta shi.‛ (Hadisini Ingantacce ne).‛ A cikin babin daga Aliyu. Mutane huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Nisa’i.‛
-
936. An karɓo daga Abi Huraira ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Kada mai zina wanda aka masa bulala yayi aure, sai misalinsa.‛ Ahmad da Abu Dawuda suka ruwaito shi, kuma mazajen hadisin Amintattu ne.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛
-
937. An karɓo daga Aishatu Allah Ya yarda da ita ta ce: ‚Wani mutum ya saki matansa saki uku, sai wani mutum ya aureta baiyi jima’i da ita ba, sai suka rabu, sai mijin farko ya naso, ya mai da matarsa, sai aka tambayi Manzon Allah ﷺ game da haka?‛ Sai ya ce: ‚A’a, sai kowa ya ɗanɗani na farko ya ɗan ɗani farjin ɗan uwa kamar yanda na farko ya ɗanɗana da farko.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.