
HASKEN MUSULUNCI
February 15, 2025 at 06:06 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
16/08/1446. Asabar.
15/02/2025. Asabar.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {175}
_______________
-
*BABIN BAYANIN HUKUNCIN ISUWA DA ZA|I DA YANDA AKE YINSA.*
-
938. An karɓo daga ɗan Umar ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Larabawa sashensu, yana isuwa wa sashe, masu walicci sashensu yana isuwa wasashe, sai mai saƙa da mai yin ƙaho.‛ Hakim ya ruwaito shi.‛ Kuma a cikin isnadinsa akwai wani mai ruwya da ba mabata ba, kuma Abu Hatim ya musanta hadisin.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne so sai).‛
Yana da shaida daga Bazzari daga Mu’azu ɗan Jabal da Isnadi yankakke.
-
939. An karɓo daga Faɗima ɗiyar ƙaisin Allah Ya yarda da ita ta ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya ce: ‚Mata ki auri Usma.‛ Muslim ya ruwaito shi.‛
-
940. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya ce: ‚Ya ku ɗiyar darare ku auri Aba Hindi, kuma ku aurar masa, ya kasance yana yin ƙaho.‛ Abu Dawuda da Hakim suka ruwaito da isnadi mai kyau.‛ (Hadisin hasanun ne).‛
-
941. An karo daga Aishatu Allah Ya yarda da ita ta ce; ‚An bada Barira zaɓi akan mijinta a lokacin da aka ‘yanta ta.‛ Bukhari da Muslim suka ruwait shio.‛
Daga Muslim Allah Ya yarda da ita ta ce: ‚Mijinta ya kasance bawa ne.‛ a cikin wuri ruwaya: ‚Ya kasance cikakken ɗiya.‛ Aamma na farko yafi tabbata.‛ Ya inganta daga ɗan Abbas Allah Ya yarda da dasu, daga Bukhari cewa: ‚Shi bawane.‛
-
942. An karɓo daga Dahhaki ɗan Fairuzul Dailami daga babansa Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Na ce: ‚Ya Manzon Allah! Na Musulnta a ƙarƙashi na akwai ni da ‘yan’uwa biyu, (wato mata
kamar macce da goggonta).‛ sai Manzan Allah ﷺ ya ce: ‚Ka sake dukkan wanda ka keso ka zauna da guda.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Nisa’i. Ɗan Hiban da Darul ƙuɗini da Baihaƙi sun inganta shi. Bukhari ya Illanta shi.‛ (Hadisin Hasanun ne).‛
-
943. An karɓo daga Salim daga babansa Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Gailan ɗan Salma ya Musulunta yana da mace goma, suka musulunta tare da shi, sai Annabi ﷺ yayi umurni ya zaɓi huɗu daga cikinsu.‛ Ahmad da Tirmizi suka ruwaito shi.‛ ɗan Hibban da Hakim suka inganta shi, Bukhari da Abu Zur’a da Abu Hatim suka illanta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.