HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 16, 2025 at 05:55 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 17/08/1446. Lahadi. 16/02/2025. Lahadi. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {176} _______________ - 944. An karɓo daga ɗan Abbas ya ce: ‚Annabi ﷺ ya mai da ɗiyarsa Zainab ga Abi Asi ɗan Rabi’u bayan shekara shida da auren, farko bai sake sabon aure ba.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi, banda Nisa’i. Ahmad da Hakim suka Inganta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛ - 945. An karɓo daga Amru ɗan Shu’aibu daga babansa daga kansa ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya mai da ɗiyarsa Zainabu ga Abil Asi da auren sabo.‛ Tirmizi ya ce ‚Hadisin ɗan Abbas yafi kyanwon isnadi, (Wato hanyan karɓo hadisin) da aiki da Hadisin Amru da Shu’aibu.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ - 946. An karɓo daga ɗan Abbas Allah Ya yarda dasu ya ce: ‚Wata mace ta musulunta yayi aure sai tayi aure, sai mijinta ya zo, sai ya ce: ‚Ya Manzon Allah! Haƙiƙa na musulunta kuma ta san musulunta na, sai Manzon Allah ﷺ ya ciro ta daga wan can mijin zuwa mijinta, na farko. Ahmad da Abu Dawuda da ɗan Maja suka ruwaitoshi. Ɗan Hibban da Hakim suka ingantacce ne.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ - 947. An karɓo daga Zaidu ɗan Ka’abu ɗan Ujara daga babansa ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya auri Aliya daga bani gifar, a lokacin da ya shiga gare ta ta sanya kayanta, a lokacin da take kwarenye tufafinta, sai ya ga alaman fari a jikinta, sai Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Mata ɗaura kayanki ki tafi ga iyalanki, sai ya bata sadakinta.‛ Hakim ya ruwaito shi.‛ A cikin isnadinsa akwai Jamilu ɗan Zaidu, kuma shi an jahilce shi, kuma an saɓani a gare shi a cikin malaman hadisinsa, saɓani mai yawa.‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments