HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 17, 2025 at 05:40 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 18/08/1446. Litinin. 17/02/2025. Litinin. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {177} _______________ - 948. An karɓo daga Sa’idu ɗan Musayyibi daga Umar ɗan Khaɗɗabi Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Dukkan mutumin da ya auri mace yayi jima’i da ita, sai ya sameta da alamar kuturta, mai kurji, ko hauka, ko kuturta marar kurji, to, tana da sadakin ta daya ambata matashi. Shi kuma ya nada abinda yayi mata ruɗi wajen manta.‛ Sa’idu ɗan Mansur da Malik da ɗan Abi Shaiba, suka ruwaito shi, kuma mazajen masu ruwayan hadisin amintattu ne).‛ - 949. An karɓo daga Sa’id kuma daga Aliyu kamarsa. Ya ƙara ya ce:d‛Ka ta na da ƙaho farjinta da akwai zaɓi idan yayi jima’i da ita tana da sadaki da yin ɗan-ɗana min farjinta.‛ - 950. Daga wata hanyar Sa’idu ɗan Musayyibu kuma: ‚Umar yayi hukunci akan mai kanƙanin zakari akan a kinkirata masa shekara. (Domin neman magani)‛. Mazajen hadisin amintattu ne. - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments