
HASKEN MUSULUNCI
February 18, 2025 at 07:47 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
19/08/1446. Talata.
18/02/2025. Talata.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {178}
_______________
-
*BABIN BAYANIN HUKUNCIN ZAMANTA KUWA TSAKANI NA MIJI DA MACE DA YANDA AKE WASU MU’AMALA NA ZAMA DA KWANCI YA DA KUMA HANI GAWASU AYYUKA WAJEN YIN JIMA’I DA SAURANSU*.
-
951. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Wanda aka la’ana shine luɗu da matar sa ta duburunta da ita.‛ Abu Dawuda da Nisa’i suka ruwaito shi, kuma lafazinsa ne.‛ (Hadisin Hasanu ne).‛
-
952. An karɓo daga ɗan Abbas Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Allah baya dubi ga mutumin da yazo wa namiji, ko mace ta duburunta.‛ Tirmizi da Nisa’i da ɗan Hibban suka ruwaito shi.‛ kuma an illanta shi da cewa Mauƙufi ne. (Hadisin ingantacce ne).‛
-
953. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Wanda ya kasance yayi imani da Allah da ranar Lahira, to, kada ya cuci maƙwafcin, kuyi wasiyya wa matanku, da alheri, domin an haliccesu ne, daga ƙashin haƙarƙari, domin abinda ya fi karkata daga ƙashin haƙarƙari, samanshi saboda haka idan ka tafi domin ka tsai da, sai ya karye, idan kuma kace zaka barshi, to, ba zai gushe ba, yana karka, to, kuyi wasiyya wa mace da alheri (wato ku zauna da su da haƙuri).‛ Bukhari da Muslum suka ruwaito shi.‛
-
954. An karɓo daga Jabir ya ce: ‚Mun kansance tare da Annabi ﷺ a cikin yaƙi a lokacin da muka zo Madina, sai muka tafi don mushiga, sai ya ce: ‚Ku dakata, sai da dare ku shiga yana nufin a lokacin isha’i domin masu yin kitso su gama wanda tafita ta dawo.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ Bukhari ya faɗa a cikin ruwaya: ‚Idan ɗayanku ya dawo daga tafiya kada ya
buga ƙofa wa matansa da dare.
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.