
HASKEN MUSULUNCI
February 22, 2025 at 07:46 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
23/08/1446. Asabar.
22/02/2025. Asabar.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {182}
_______________
-
971. An karɓo daga Abdullah ɗan Amir ɗan Rabi’a daga babansa Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya halatta auren mace da takalama biyu, (domin rashi) .‛ Tirmizi ya ruwaito shi, ya inganta shi an yi kuma saɓanin cikin haka.‛ (Hadisin dwa’ifi ne).‛
-
972. An karɓo daga Sahal ɗan Sa’adu Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Annabi ﷺ ya ɗaurawa wani mutum aure da wata mace, akan zobe na baƙin ƙarfe.‛ Hakim ya ruwaito shi.‛
-
973. An karɓo daga Aliyu Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Sadaki baya kasancewa mafi ƙarancin Dirhami goma.‛ Darul ƙuɗini ya ruwaito shi, Mauƙufi.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛
-
974. An karɓo daga Uƙuba ɗan Amir Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ yace: ‚Mafi alheri sadaki, kaɗan ɗinsa.‛ Abu Dawuda ya ruwaito shi, Hakim ya inganta shi.‛ (Hadisin Ingantace ne).‛
-
975. An karɓo daga Aishatu Allah Ya yarda da ita ta ce: haƙiƙa Amrata ɗiyar Jauni ta nemi tsari daga Manzon Allah ﷺ a lokacin da aka shigar da ita gareshi, tana nufin a lokacin da ya aureta, sai ya ce: haƙiƙa kin nemi tsari da abinda ake neman tsari dashi, sai ya saketa ya umurce Usma ya yi mata kyauta da tufafi uku.‛ ɗan Majah ya ruwaito shi.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ Asalin ƙissar a cikin Sahih ne daga hadisin Abi Asaid Sa’idi.‛
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.