HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 23, 2025 at 05:58 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 24/08/1446. Lahadi. 23/02/2025. Lahadi. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {183} _______________ - *BABIN BAYANIN HUKUNCIN WALIMA DA YANDA AKE YI DA ABIN DA AKA HANA.* - 976. An karɓo daga Anas ɗan Malik Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya ga alamar ƙunshi ga Abdurrahaman ɗan Aufin, sai ya ce: ‚Mene ne wan nan?‛ ‚Sai ya ce: ‚Ya Manzon Allah! Ni na yi auren mace, akan Ma’aunin nawat na dinari, ya ce, masa: ‚Allah ya sa maka albarka, kayi walima, ko da akuya.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 977. An karɓo daga ɗan Umar Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Idan aka kira ɗayanku zuwa walima ya tafi.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ A ruwayar Muslim: ‚Idan ɗayanku ɗan’uwansa ya angwance ne, ko waninsa.‛ - 978. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Mafi sharrin Abinci, abincin walima, wanda ake hana a ga wanda ya zo gareta, ana bada wanda bai zoba: wanda bai amsa kiran ba, haƙiƙa ya saɓawa Allah da ManzonSa: Muslim ya ruwaito shi.‛ - 979. An karɓo daga gareshi Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Idan an kira ɗayanku ya amsa, idan yana azumi yayi sallah, idan ba yayin azumi, to, yaci abinci.‛ Muslim ya ruwaito shi.‛ Daga hadisin Jabir kamarsa: ‚Ya ce: ‚Idan yaso yaci, idan yaso ya bari.‛ - 980. An karɓo daga ɗan Mas’ud ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Abincin walima a rana farkowajibi ne, kuma abincin rana na biyu sunna ce, kuma abincin yini na uku jiyar wane, wanda ya jiyar, Allah zai jiyarma da shi.‛ Tirmizi ya ruwaito shi.‛ (Hadisin dwa’ifi ne).‛ Yana da shaida ga Anas daga ɗan Maja.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ - 981. An karɓo daga Safiyya ɗiyar Shaiba Allah Ya yarda da ita ta ce: ‚Annabi ﷺ yayi walima ga wasu sashen matansa, da mudu biyu, na shair.‛ Bukhari ya ruwaito. - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments