
HASKEN MUSULUNCI
February 24, 2025 at 07:10 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
25/08/1446. Litinin.
24/02/2025. Litinin.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {184}
_______________
-
982. An karɓo daga Anas ya ce: ‚Annabi ﷺ ya tsaya a tsakanin Khaibara da Madina Miluku, yana kwanada Safiyya, sai na kira Musulmai, zuwa walimarsa, babu komai cikinsa, kamar waina, da nama, babu komai sai yayi umurni, aka shinfiɗa shinfiɗa, sai ya jefa dabino da cikwu da kitse a kanta.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛
-
982. An karɓo daga wani mutum daga Sahaban Annabi ﷺ ya ce: ‚Idan aka kira mutum a wurin walima biyu, to, ya tafi ƙofar, mafi kusa, amma idan akwai wanda ya riga, to, ya tafi wanda ya riga gayyatansa.‛ Abu Dawuda ya ruwaito shi. Isnadinsa Mai rauni.‛ (Hadisin dwa’ifi ne).‛
-
983. An karɓo dag Abi Juhaifa Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚ Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ba’a cin abinci a kishinkiɗe.‛
-
984. An karɓo daga Umar ɗan Abi Salma ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Min ya ƙaramin yaro! Ka anbaci Allah, sa’an nan kuma ka ci abinci hannun damanka, kuma ka ci abinda ke gaban ka‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛.
-
986. An karɓo daga ɗan Abbas ya ce: ‚Lallai an zo wa Annabi ﷺ da kwaryan abinci, sai ya ce: ‚Ku ci gafensa, kuma kada ku ci tsakiyansa, domin albarka tana sauƙa a tsakiyrsa‛. Mutune huɗu ne suka ruwaito shi‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛.
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.