
HASKEN MUSULUNCI
February 25, 2025 at 07:35 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
26/08/1446. Talata.
25/02/2025. Talata.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {185}
_______________
-
987. An karɓo daga Abi Huraira ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ bai taɓa aibanta wani abinci ba, daidai da rana ɗaya. Kuma ya kasance idan yayi sha’awar wani abu, sai yaci shi, idan kuma yaƙi sai ya bar shi‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛.
-
988. An karɓo daga Jabir Allah Ya yarda da shi daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Kada ku ci da haguna, domin lallai shaiɗan yana ci da haguna ne‛. Muslim ne ya ruwaito shi‛.
-
989. An karɓo daga Abi ƙatada, Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Idan ɗayanku zai sha (ruwa), to, kada ka ya yi nunfashi cikin ƙwaryar (ruwa)‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛.
-
990 An karɓo daga Abi Dawuda daga ɗan Abbas Allah Ya yarda da su kamarsa, sai shi ya ƙara da cewa: ‚Kada yayi busa cikin sa‛. Kuma Tirmizi ya inganta shi‛.
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.