HASKEN MUSULUNCI
March 1, 2025 at 08:24 PM
*_Assalamu Alaikum_*
"
" *_18/08/1438_*
" *_15/05/2017_*
"
*_TSARABAR MAI AZUMI_*
"
*_DARASI NA (001)_*
*...........................................................*
"
*GABATARWA!!!*
"
Da sunan Allah mai Rahma mai jinqai, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, wanda ya wajabta wa bayinsa azumtar watan Ramadana mai albarka, da fadinsa cewa:- _*`Ya ku wadanda kukayi imani, an wajabta maku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabaceku, ko kunji tsoron Allah,*/tsammanin ku kuyi wa Allah tsan-tsar biyayya, ,'(suratul baqarah, aya ta 223)
"
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam wanda yake cewa:- *An gina musulunci Akan abubuwa guda biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawansa ne, kuma manzo, tsaida sallah, Bada zakkah, yin azumin watan Ramadan, ziyartar dakin Allah mai alfarma.* (Imamu Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).
"
Bayan haka, sabida irin alkhairan da wannan watan ya tattaro da Rahma da gafara, da 'yanci, da jinqai, da saukar mala'iku, da bude kofofin Aljannah, da rufe kofofin wuta, da daure shaidanu, da saukar Alqur'ani mai tsarki acikinsa, shine naga yakamata na kara fito da wasu daga cikin falalolin da wannan watan yake dauke dasu, don amfanuwa ga 'yan uwa musulmai.
"
Ina fatan Allah madaukakin sarki ya sawa wannan littafi albarka, yakuma amfani duk wanda ya karantashi, Amin.
"
Allah yasa mudace duniya da lahira Ameen.
"
"
*Wallah A,alam*
"
"
_Muhadu a darasi nagaba inshaa Allahu_.
"
"
*_DAGA_*ZAUREN
*_HASKEN MUSULINCI_*
_*08133045868*_