Sirrin rike miji
February 26, 2025 at 07:24 PM
Fitar Farin Ruwa ga Mace ko Namiji Wanda Baya Wari
Fitar farin ruwa daga al'aura ba wani abu ne da ya zama matsala ba, sai dai idan yana da wasu alamomi masu nuna matsala. Ga bayani kan kowanne:
A Wurin Mace
Farin ruwa mara wari a wurin mace yawanci ruwan al’ada ne da ake kira discharge.
Yana taimakawa wajen tsaftace farji da kuma kiyaye danshi.
Idan yana da laushi kamar egg white, yana iya nuna cewa kina kusa da lokacin ovulation (lokacin da mace ke iya daukar ciki).
Idan yana da kauri kamar madara ko yana hade da zafi, ƙaiƙayi, ko wari, yana iya nuna cuta kamar infection.
A Wurin Namiji
Idan namiji yana fitar farin ruwa marar wari, yana iya zama pre-ejaculate (maziyy), wanda ke fitowa kafin inzali a lokacin da yake jin sha’awa.
Idan yana yawan fitowa ba tare da jin sha’awa ba, yana iya zama alamar matsalar prostate ko infection.
Ya Ya Za a Yi?
Idan ruwa ne na al'ada kuma babu wata matsala kamar wari, ƙaiƙayi, ko zafi, ba wata damuwa.
Idan yana da wari, yana da yawa sosai, ko yana tare da ciwo, yana da kyau a je asibiti.
Tsafta da cin abinci mai kyau na iya taimakawa wajen rage yawan fitar ruwan.
👍
❤️
🙏
18