Sirrin rike miji WhatsApp Channel

Sirrin rike miji

20.6K subscribers

About Sirrin rike miji

🌿 Barka da Zuwa WhatsApp Channel ɗinmu! 🌿 Maraba da ku zuwa wannan tasha, inda za ku samu ingantattun bayanai game da magunguna a Musulunci, lafiya, da hanyoyin kula da jiki bisa tsari na sunnah. ⚠ Ka’idojin Channel: ✅ Duk bayanan da ake wallafawa suna da tushe. ✅ Za ku iya tambaya ta rubutu kawai. ❌ Banda Voice Note ko kira. Ku kasance da mu don ilmantarwa da fa’idodi masu amfani! 📌 WhatsApp: ☏+2348037538596/08066627317

Similar Channels

Swipe to see more

Posts

Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 4:25:13 PM

Barinmu kowace mace ta yi aure, domin duka mata ƴan'adam ne, babu wadda ta rako mata duniya. Yawan adadin mata sama da maza (surplus of women) matsala ce da kusan kowace ƙasa ta duniya take fuskanta a yau. Alhamdu lilLah da ni'imar musulunci, domin shi ne addinin da ya magance wannan matsalar, ta hanyar halattawa maza auren mace fiye da ɗaya har zuwa huɗu. Idan muka duba al'ummarmu, akwai mata dayawa, ƴan mata da zawarawa, suna son aure, domin suma mutane ne kamar kowa, suna da buƙata koda ba su faɗa ba, don haka dole ne mu ƙarfafa gwuiwar maza masu hali da su ƙara aure, domin raya sunnar Annabi ﷺ da warware matsalar al'umma. Su kuma matan da suke daga ciki su yi haƙuri, duk da cewa rauni da kuma son rai ba zai bari su gamsu da maslahar ƙarin aure ba. Kowace mace tana son ƴan'uwanta su yi aure, ƴaƴanta mata su yi aure koda a matsayin kishiyar wata ne, amma ba ta son mijinta ya auri wata. Babu wani wa'azi a duniyar nan da zai gamsar da mata su karɓi kishiya, kuma fa dukkansu mata ne, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne! A yayin da muke kira da maza masu hali da su ƙara aure, muna kiransu da su riƙa kamanta adalci da kuma halacci, kada su manta da alherin baya. Amma kada wani alherin uwargida ko kyautatawarta ko kirkinta ya hana ka yi mata kishiya, haka nan kada barazana ko tausayi ya hana ka yi mata kishiya. Ka sanya a ranka ƙarin aure haƙƙinka ne, ba ka yi wa kowa laifi ba don ka ƙara aure, kai dai ka yi adalci, sa'an nan a lallaɓa uwargida, a yi mata kyaututtuka na dannin ƙirji. - Isa Sadi

👍 ❤️ 🙏 😠 😢 🥰 16
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 4:23:45 PM

Idan ka iya soyayya duk kudin me kudi bazai kwaceta a wajen ka ba!

👍 ❤️ 🙏 😂 14
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 5:45:22 PM

Ki Auri Namijin da Yafi Sonki fiye da Yadda Kike Sansa Ana cewa mace ya kamata ta auri namijin da yafi sonta fiye da yadda take sansa. Ba don cewa bata cancanci soyayya mai zurfi ba, amma domin namiji wanda yake kaunarta da gaske ba zai taɓa daina nuna hakan ba. Zai daraja kasancewarta, ya kare zuciyarta, kuma ya sa ta ji tana da daraja a kowanne rana. Namiji wanda yafi sonki zai: ✨ Ba ki muhimmanci a kowanne fanni, Ba wai kawai zai faɗa miki kina da muhimmanci ba, zai nuna hakan ta ayyukansa. ✨ Zai sa dangantakarku ta kasance mai sauƙi, Babu wasa, babu ruɗani, soyayya ce mai sauƙin fahimta da tafiya. ✨ Yi fafutuka saboda ke, ba tare da gajiyawa ba, Zai fi son zaman lafiya, fahimta, da sulhu fiye da gardama marar amfani. ✨ Zai Kasance mai aminci da tsantseni, Ba zaki taɓa shakkar niyyarsa ba, domin ayyukansa za su tabbatar miki da hakan kowacce rana. ✨ Kwanciyar hankali a jiki, da soyayyarsa za ta zama mafakarki. Idan namiji na sonki fiye da yadda kike son sba zai taba gajiya ba. Zai dinga kula da ke da haƙuri, da girmamawa, da ci gaba, yana tabbatar da cewa soyayyarsa ba kalmomi ba ne kawai, amma hanya ce ta rayuwa da zai kula da zumuncinku. Ba ina nufin mace bai kamata ta so mijinta da gaske ba, soyayya ya kamata ta kasance mai daidaito. Amma idan soyayyar namiji tafi, hakan yana tabbatar da cewa ba zai taɓa raina ki ba, ba zai daina zaɓar ki ba, kuma ba zai daina sa ki jin ke ce mafi muhimmanci a duniyarsa ba. Ki Auri namijin da yake kallonki kamar ke ce albarkarsa mafi girma.

👍 ❤️ 🙏 🤲 👌 38
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 4:33:05 PM

HALAYYAR DANKA ** MADUBIN HALAYYARKA NE ■ Danka ya cika karya da yawa ** Ma’ana kana tsananin bin diddiginsa. ■ Danka ba shi da karfin zuciya ** Ma’ana ba ka karfafa masa gwiwa. ■ Danka bai iya magana ba ** Ma’ana ba ka yin hira da shi. ■ Danka yana sata ** Ma’ana ba ka koya masa yin kyauta ba. ■ Danka matsoraci ne ** Ma’ana kana yawan kare shi. ■ Danka ba ya ganin girman mutane ** Ma’ana kana yawan daka masa tsawa. ■ Danka kullum cikin fushi ** Ma’ana ba ka yabonsa. ■ Danka marowaci ne ** Ma’ana ba ka sanya shi cikin al’amuranka. ■ Danka yana cin zalin mutane ** Ma’ana kai mai kaushin hali ne. ■ Danka yana da rauni ** Ma’ana kana yawan yi masa barazana. ■ Danka ya cika kishi ** Ma’ana ba ka kula da shi. ■ Danka yana yawan damunka ** Ma’ana baka rungumarsa ka sunbance shi. ■ Danka ba ya yi maka biyayya ** Ma’ana ka cika yawan ba da umarni. ■ Danka ba ya shinga mutane ** Ma’ana ka shagalta da yawa. ~~ In ji: Dr. DARIK AL HABIB

👍 🙏 🤔 😮 12
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 3:50:43 PM

Ance dai ta farko cousin ce, ko biyayyar iyaye ko kuma family friends, ta biyu ta soyayya they feel anfi son su, ta uku yar ramakon uwar gida, ta hudu cike gurbi. ☕️

😂 😢 👍 😮 🤷‍♀️ 12
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 4:45:20 PM

Kin taba mamakin abin da ya sa maza suke mutuwar son wasu matan? Sabida wadancan da ake so, basu cika gaggawa da iya yi bane.😁

👍 😂 ❤️ 🙏 24
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 7:20:42 PM

Ku samu KARON 'BAURE a hada da BAWON RUMMAN sannan a samo SAIWAR KANKANA, a samo GERON MATA shima a hada aciki, saikuma a samo SAIWAR SANYA a hada aciki da KANINFARI DA CITTA... Ku hadasu guri daya sannan a niqa su su zama gari yayi laushi sosai. Za'a dinga diban cokali daya kullum ana zubashi cikin ruwan zafi ko shayi ana sha, kullum sau daya... Ga mata Yana yin matsi na ciki sosai, sannan zai magance sanyi kuma ya samar da ni'ima. Ga maza kuma, yana inganta lafiyar jiki sannan ya kori dukkan datti na mara kuma ya kara lafiya ga al'aura in sha Allah. Ku jarraba wannan Yaya Mustyn ku Mallam Mustee

👍 6
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 7:19:41 PM

MAGANIN CIWAN KODA SAHIHI DA YARDAR ALLAH, A GWADA AGANI. Idan kun san wanda ke da matsalar koda, Wannan shine abin da suke bukata suyi. 1. A samo ganyen yalo 2. A Tafasa ganyen 3. A Bar shi yayi sanyi 4. Ana shan ruwan safe da rana da dare 5. Sakamakon yana da ban mamaki. Da fatan za'a yi share don taimakawa mutanen da suke cikin irin wannan yanayin su amfana. ALLAH Ya Bamu Lafiya ya Cigaba da Inganta mana Ita.

👍 ❤️ 🙏 6
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 4:03:01 PM

Samsung or Iphone👀?

Post image
1⃣ ❤️ 1️⃣ 👍 💛 🙏 9️⃣ ☑️ 🍏 34
Image
Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
6/9/2025, 3:44:13 PM

Idan namiji ya bata maki rai, ba blocking ko dogon wasikar tuhuma cikin fushi zaki ba... Shuru yafi komai. Zai yi nadama.🤔

👍 😢 🙏 💯 😮 20
Link copied to clipboard!