Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
February 28, 2025 at 06:11 AM
#falalar_aure Manzon Allah ﷺ yace : " Wanda Allah ya arzuta shi da samun mace ta gari , to haƙiƙa Allah ya taimake shi a kan rabin addinin sa , to yaji tsoron Allah a sauran rabin." ) رواه طبراني في « الأوسط » 294 / 1 ، والحاكم في” مستدركة “ 175 / 2 ) FA'IDA : Arziki ne babba wanda Allah ya baka na samun mace ta gari to kayi ƙoƙari ka cika rabin addinin ka , idan Allah ya baka mace ta gari to ya hanaka daga yin Zinah da kuma bin mata dan haka ka gode ma Allah. _ Allah Subhanahu Wata'ala ya arzuta mu da samun irin wannan macen Allah bamu mace ta gari wadda idan mun kalle ta zamu yi farin ciki kuma mu kiyaye duk wani abu da zai saɓama Allah subhanahu wata'ala, Matan ma Allah basu maza na gari masu ƙaunar tsakani da Allah. #darussan_mace_ta_gari
❤️ 👍 🙏 5

Comments