Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
February 28, 2025 at 06:12 AM
Assalamu Alaikum KAIKAYI MAI KAMAR TAFIYAR KIYASHI A JIKI (FORMICATION) Jin kaikayi kamar kwaro yana yawo a karkashin ko saman fatar jikin mutum shi ake kira “formication” a likitance. An samo Kalmar ne daga “formica” a harshen Latin na kasar Rome, wacce take nufin tururuwa (ant). Kaikayin yakan zo ta siga daban-daban. Yana iya kasancewa jin tsikari (tingling), ko jin waiwayi (sensation), ko jin kaikayi (itching), ko jin radadi (burning). Wani lokaci kuma yakan zamo daukewar jin motsi gaba daya idan aka taba fatar mutum (numbness), watau mutum yaji kamar ba jikinsa aka taba ba. Abinda aka sani shine ana jin kaikayi ne idan wani abu ya taba fata. Amma idan jin tafiyar kiyashi a jiki ne, to, mutum zai ji kaikayi alhalin babu abinda ya taba fatarsa. Ma’ana, zuciyarsa ce take riya masa cewa wani abu yana yawo a saman fatarsa ko karkashin fatarsa, don haka sai ya rika jin kaikayi. Irin wannan kaikayin yakan haifar da rashin jin dadi tare da soshe-soshen jinki, har yakai ga yima fata rauni ba tare da daina jinsa ba. RABE-RABEN KAIKAYIN TAFIYAR KIYASHI A JIKI Kaikayin tafiyar kiyashi a jiki ya rabu gida biyu kamar haka: 1. Tafiyar kiyashi a jiki na rudanin kwakwalwa, wanda yake faruwa ba tare da wata matsala ta rashin lafiya ba amma mutum ya riya a zuciyarsa kamar kwaro yana bin jikinsa. A likitance ana kiransa “primary delusional infestation”. 2. Tafiyar kiyashi a jiki wanda wata rashin lafiya ko kuma wani yanayi da mutum ya sami kansa a ciki yake haddasawa. A likitance ana kiransa “secondary delusional infestation”. Primary da secondary delusional infestations din suna aukuwa ne idan aka sami rashin daidaiton wani sinadari mai suna “dopamine” a cikin kwakwalwa. Shine yake da alhakin aika sako daga kwakwalwa zuwa sassan jiki domin yin motsi, tunani, nishadi, damuwa, da sauransu. Saboda haka ake kiransa “neurotransmitter hormone”, watau dan sakon sinadari. Anan zamu fahimci cewa tafiyar kiyashi a jiki tana kasancewa a dalilin matsalar kwakwalwa (psychiatric disorder), ko rashin lafiya (underlying medical condition), ko kuma amfani da kwayoyin magani (drug and medication use). TAFIYAR KIYASHI A JIKI DALILIN MATSALAR KWWAKWALWA Matsalar kwakwalwa (psychiatry) a likitance ba tana nufin ciwon hauka bane. A’a, wani fanni ne na ilimin lafiya wanda ya shafi ganowa da magance matsalolin hankali (mentality), tunani (memory), shu’uri (emotion), da sauransu. Tafiyar kiyashi a jiki dalilin matsalar kwakwalwa ya kunshi: 1. Damuwa (depression): Tana sanya mutum ya rika jin bacin rai mai tsanani ba tare da anyi masa wani abu da ya cancanci ya bata masa rai ba. Hakan zai sanya mutum ya daina sha’awar komai a rayuwarsa, har ya rika tunanin cutar da kansa ko kuma wani makusancinsa. Mutum yakan gane cewa yana da matsalar damuwa idan ya dauki tsawon makonni biyu ko fiye da haka yana jin bacin rai babu kakkautawa. Damuwa na sanya mutum ya rika jin tafiyar kiyashi a jikinsa. 2. Jin tsoro (anxiety): Shine mutum ya rika jin fargaba da bugawar zuciya kamar wani mummunan abu zai faru da shi. Yakan faru ne a dalilin matsalar talauci, rashin masoyi, halakar dukiya, rashin aikin yi, da sauransu. Jin tsoro yana sanya mutum ya rika jin tafiyar kiyashi a jikinsa. 3. Rudewa (schizophrenia): Matsala ce ta kwakwalwa wacce take sanya tunanin mutum ya rikice ya rika gane-gane, ko mafarkai, ko sambatu. Rudewa tana sanya mutum ya rika jin tafiyar kiyashi a jikinsa. TAFIYAR KIYASHI A JIKI DALILIN RASHIN LAFIYA Akwai rashe-rashen lafiya wadanda suke da alaka da lakar jiki (neurological illnesses) da zasu iya haddasa jin tafiyar kiyashi a jiki. Sun kunshi: 1. Parkinson’s disease: Ita ce cutar rawar jiki, watau jikin mutum ya rika kyarma. Wani lokaci kuma sai jiki ya sandare ya daina motsi. 2. Dementia: ita ce cutar yawan matuwa da dimaucewa. 3. Traumatic brain injury: Shine samun rauni a kwakwalwa sakamakon bugewa ko hadarin da ya shafi kai. 4. Stroke: Shine mutuwar ko kuma shanyewar tsagin jiki. Yana aukuwa a dalilin hawan jini mai tsanani. 5. Meningitis: Shine ciwon sankarau, wanda yake kama lakar wuya da baya (spinal cord) kuma ya sanya jikin mutum ya sandare. 6. Multiple sclerosis: Cuta ce ta kwakwalwa da laka, wacce take haifar da rashin gani, kasala, da radadi a jiki. 7. Huntington’s disease: Cuta ce wacce ake iya gadonta, kuma tana haddasa lalacewar kwayayen halittar kwakwalwa da laka. 8. Delirium: Cuta ce ta kwakwalwa wacce take sanya rashin magana, rashin barci, gane-gane, da rudewa. 9. Chronic liver or kidney disease: Ciwon koda ko hanta wanda yayi tsanani. 10. Cancer: Ciwon sankara, kamar sankarar jini da sauransu. 11. Infections: kamuwa da kwayoyin cuta kamar ciwon sanyi, HIV, ciwon sugar, da sauransu. 12. Karancin jini, da kuma karancin wasu sinadarai a jiki kamar vitamin B12. 13. Perimenopause: Kusantowar daukewar jinin al’ada ga macen da shekarunta suka fara nisa. TAFIYAR KIYASHI A JIKI DALILIN ANFANI DA KWAYOYIN MAGANI Yin amfani da kwayoyin maganin kara kuzari ga masu yin wasannin motsa jiki da kuma shan kayan maye kamar cocaine, giya, wiwi, yana iya haddasa jin tafiyar kiyashi a jiki. Wadannan su ake kira “recreational drugs”, domin ana shan su ne ba domin a magance wata cuta ba, sai domin bukatar jin tasirinsu kawai a jiki. Haka nan wadansu daga cikin kwayoyin da ake sha domin magance cututtuka watau “prescription drugs” suna haddasa jin tafiyar kiyashi a jiki. Kadan daga cikinsu sune: 1. Methylphenidate (Ritalin) wanda ake amfani da shi wajen magance matsalar rashin natsuwa (attention deficit hyperactivity disorder - ADHD). 2. Antibiotics kamar ciprofloxacin da clarithromycin wandanda ake amfani da su wajen magance cututtukan numfashi (respiratory tract infections), cututtukan mafitsara (urinary tract infections), cututtukan sanyi (sexually transmitted infections), cututtukan narkewar abinci (digestive tract infections), da sauransu. 3. Antidepressants (citalopram, fluoxetine, escitalopram etc.) wadanda ake amfani da su wajen magance cututtukan damuwa. 4. Corticosteroids (dexamethasone, hydrocortisone, methylprednisolone, etc.) wadanda ake amfani da su wajen magance cututtukan kumburi. MAGANCE JIN TAFIYAR KIYASHI A JIKI (TREATMENT OF FORMICATION) Magance jin tafiyar kiyashi a jiki ya danganta da dalilin da ya haddasa shi. Idan cututtukan kwakwalwa ne, to, dole sai anga likitan kwakwalwa. Idan shan recreational drugs ne ya haddasa shi, to, dole sai an dai na amfani da su. Haka kuma idan laulayin shan prescription drugs ne (side effects) ya haifar da shi, to shima sai a daina amfani dasu, misali kaikayin da chloroquine ke haddasawa. Idan kuma karancin sinadarai a jiki ne, to, sai a rika cin wadatacce, kuma ingantaccen abinci. Idan kuma wata rashin lafiya ce cikin wadanda na lissafa a sama, to, sai a magance ta. Idan kuma kusantowar daukewar al’ada ne ya haddsa shi, to, sai a rika shafa mayuka wadanda zasu samar da damshi a jikin fata. WalLahu A’lam. By Usman shehu
👍 3

Comments