Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
February 28, 2025 at 04:31 PM
🌿 AMFANIN SABAYA GA MACE 🌿 Sabaya na daya daga cikin abubuwan da ke inganta lafiyar mace, musamman bayan haihuwa. Ga wasu daga cikin fa’idodinsa: ✅ Taimakawa wajen dawo da halittar mace – Yana hana jikin mace faduwa ko sauyawa bayan haihuwa, kuma yana tabbatar da cewa nononta ba zai zube ba. ✅ Jikinta zai yi laushi da santsi – Sabaya na sa fata ta yi taushi da santsi kamar kwalabiya. ✅ Kare mace daga ramewa bayan haihuwa – Yana cike gibin da mace ke samu bayan haihuwa, yana hana ta ramewa fiye da kima. ✅ Yawan ruwan nono da ingancinsa – Sabaya na kara yawan ruwan nono, yana kuma hana shi lalacewa. ✅ Kiwon lafiya ga jariri da magidanci – Jaririn da aka haifa zai samu kariya daga cututtuka, kuma magidanci idan ya sha yana kara lafiya da kuzari, har ma wajen kusantar iyalinsa. --- 📝 ABUBUWAN DA AKE BUKATA WAJEN HADA SABAYA 🔹 Alkama – 1 Mudu 🔹 Danyen Shinkafa – 1 Mudu 🔹 Waken Suya – 1 Mudu 🔹 Ridi – ½ Mudu 🔹 Hulba – ½ Mudu 🔹 Gyada mai bargo/Kamfala 🔹 Madara 🔹 Zuma --- 🔄 YADDA AKE HADA SABAYA 1️⃣ Soyawa da Jikewa: A soya ridin har sai ya yi kantu. A soya gyada har sai ta yi irin ta ƙuli-ƙuli. A jika shinkafa da alkama na tsawon 5 hours, sannan a shanya su su bushe. 2️⃣ Nika: A hade ridi, gyada, alkama, hulba da shinkafa sannan a niƙa su tare har su zama gari. 3️⃣ Amfani: Ana iya fara ba mace tun tana da ciki har zuwa bayan haihuwa don lafiyarta da ta jaririnta. Yana tabbatar da cewa nononta zai kasance da kyau, ko da tana shayarwa ko a’a. --- 🥛 YADDA AKE SHA A dama shi kamar yadda ake kunu, amma idan aka zuba ruwan zafi, ana iya maida shi kan wuta dan ya dahu sosai. Mace kadai: Cokali uku a rana, a haɗa da zuma da madara (babban cokali). Idan za a sha tare da magidanci: A sanya cokali shida. > ⚠️ Shawara: Ana iya sha safe da yamma domin samun kyakkyawan sakamako. Allah ya sa albarka, ya kuma ba da lafiya da ingantacciyar rayuwa! 🌸 #gyaran_nono #drabdulwahab #sirrinrikemiji #sabaya #sabaya_gyaran_nono #maganin_gyaran_nono
❤️ 👍 2

Comments