
Sirrin rike miji
March 1, 2025 at 09:55 AM
Maganin Gyaran Nono na Mata – Karin Girma, Ragewa da Mikarwa
SHARE 🌾
Domin gyaran nono ga mata
Idan baku mantaba, mun yi muku alkawari cewa za mu kawo muku bayani akan yadda za ku magance matsalar zubewar nono, musamman ga mata masu shekaru 39 da ƙasa.
Saboda mahimmancin gyaran jiki ga mata, musamman gyaran nono, mun kawo muku bayanai akan nau’ikan gyaran nono, wanda ya kasu kashi uku:
🌾 Kashi na farko: Karin girman nono.
🌾 Kashi na biyu: Rage girman nono.
🌾 Kashi na uku: Mikar da nono.
Mun riga mun yi bayani akan karin girman nono. Yau kuma za mu yi bayani akan yadda za a magance matsalar zubewar nono a wajen mata masu ƙarancin shekaru. Sai dai har yanzu muna bin bashin bayani akan rage girman nono, wanda za mu kawo nan gaba, In Sha Allah.
Matsalar Zubewar Nono
Hakikanin gaskiya, kowace mace tana son ta ga tana da tsayayyen nono tsawon rayuwarta. Amma kash! Hakan ba mai yiwuwa bane gaba ɗaya, domin zubewar nono dabi’a ce da ke faruwa tare da tafiyar shekaru.
Dalilan da ke haddasa zubewar nono:
🤰 Shayarwa
🤰 Daukar ciki
🤰 Yankewar jinin haila gaba ɗaya
🤰 Ramewa cikin dan kankanin lokaci
🤰 Kiba mai yawa
🤰 Wasu cututtuka kamar kansa (cancer) da sauransu
Hanyoyi 3 na Mikar da Nono Cikin Sauƙi
Domin magance matsalar zubewar nono ba tare da wahala ko kashe kuɗi ba, ga hanyoyi uku da za a bi:
1. Amfani da Kankara
Samu kankara, sai a shafa a nonuwa duka biyu.
A shafa ahankali har ta ko’ina na tsawon minti 2-3.
A maimaita hakan na tsawon kwanaki.
Kankara tana da tasiri sosai wajen matse nono da hana shi zubewa.
Bayan haka, a saka bra mai kyau da dacewa da jiki.
2. Amfani da Man Zaitun
A shafa man zaitun a nono kullum safe da yamma.
A shafa ahankali tare da murzawa.
Bayan haka, a saka bra da ya dace da mace.
Za a iya amfani da zaitun Lawz ko jojoba oil idan babu man zaitun.
3. Amfani da Hadin Neem Oil da Ruman
A hada neem oil da garin ruman (cokali 1).
A daura akan garwashi na ɗan lokaci har ya ɗan yi zafi kaɗan.
A sauke, a bari ya huce.
Sai a shafa a nono sau biyu a rana na tsawon kwanaki.
Kammalawa
Za a iya amfani da kowace daga cikin waɗannan hanyoyi guda uku domin magance matsalar zubewar nono. Kowanne daga cikinsu yana da tasiri sosai, In Sha Allah.
SHARE & LIKE 🔔
👍
❤️
6