
Sirrin rike miji
March 1, 2025 at 06:05 PM
Hukuncin Fitar da Maniyyi ta Hanyar Istimna’i ga Mai Azumi
════════════════
Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Malam, tambayata ita ce: Menene hukuncin azumin wanda maniyyi ya fita masa ta hanyar istimna’i?
Amsa
════════
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Akwai sabani tsakanin malamai kan hukuncin mutumin da ya fitar da maniyyi ba ta hanyar jima’i ba yayin da yake azumi. Amma mazhabar Malikiyya ta tafi akan cewa:
Wanda ya fitar da maniyyi a cikin azumi ta hanyar jin daɗi—ko ta kallon haram, ko runguma, ko tunane-tunane, ko kuma ta jima’i—azuminsa ya karye. Idan azumin watan Ramadana ne, dole ne ya rama kuma ya yi kaffara.
Kaffarar nan kuwa tana da hanyoyi uku, wanda dole sai ya zaɓi ɗaya daga cikinsu:
1. 'Yantar da bawa ko baiwa.
2. Ciyar da miskinai sittin (60).
3. Yin azumi sittin (60) a jere bayan an rama wanda aka karya.
Hukuncin nan yana da tushensa daga hadisi ingantacce da ke cikin Sahihu Muslim.
Wasu malamai, kamar Imam Ahmad, suna ganin cewa azumin kadai za a rama, tunda maniyyi ya fita ba ta hanyar jima’i kai tsaye ba.
Sai dai abu mafi muhimmanci ga wanda ke aikata istimna’i a cikin watan Ramadana shi ne ya fahimci cewa yana wulakanta alfarmar wannan wata mai daraja. Wannan kuwa babban laifi ne.
A cikin ayar da Allah ya wajabta azumin Ramadana, Ya bayyana cewa manufar azumi ita ce samun tsoron Allah:
"Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku, domin ku ji tsoron Allah."
(Suratul Baqara: 183)
Tsoron Allah kuwa yana nufin kiyaye umarninsa da haninsa, tare da yin guzuri mai kyau don ranar lahira, da kuma tuna girman Allah da kasancewarsa mai kallon bayinsa a kowane lokaci.
Wanda yake aikata istimna’i a cikin wannan wata mai albarka yana nuna cewa bai damu da tsoron Allah ba, kuma ya zaɓi hanyar da ba daidai ba. Allah Ya tsare mu daga irin wannan.
Wallahu A’alam.
🙏
👏
👍
😮
15