Hikaya
Hikaya
February 7, 2025 at 01:32 PM
Asabe Reza 1 | Hikaya Bata taɓa tsanar wata halitta a duka duniya irin Ashana ba, ita ta ƙarɓi muƙamin da nata ne, haƙƙinta ne a matsayinta na 'ya ɗaya tilo ga Kankana, ita ya da ce ta ƙarbi dukkan ragamar gidan, amma Ashana ta mata karan tsaye, ta rabata da duka burinta, yarinya ƙarama da aka kawo a kan idonta, abu ne mai girman da ba za ta taɓa bari ba. Da girman wanda ya halicceta daga gudan jini, zuwa tsoka, zuwa abin da take yanzu ta yi rantsuwa. Ashana ba za ta taɓa jindaɗi ba har cikin kabarinta. Da girman wanda ya halicceta domin bautarsa ta sake rantsuwa, sai ta mata abin da za ta ji zafi da raɗaɗin da take ji a duk ɗora ido da za ta yi kanta, sai ta fahimtar ta yadda ba ta ƙaunar kwanciyar hankalinta ko da na motsawar tsinken agogo kan babban ɗigonsa ne. Sai ta ɗaiɗaita rayuwarta ta ɓatar da tarihinta tamkar ɓacewar Allura tsakiyar teku. https://hikaya.bakandamiya.com/asabe-reza-1/
👍 ❤️ 3

Comments