Hikaya
Hikaya
February 8, 2025 at 07:47 AM
Zuciya 1 | Bakandamiya Hikaya Hayaniya ce kawai ke tashi ƙofar gidan, matasan fulanin maza faɗi suke, a fito da Nafi su ƙona ta. Inna Hure ce ta leƙo tana masifa, “Ku je ku neme ta wani wuri bubu ita nan”. Ɗaya daga cikin matasan ya ce “A fito mana da ita ko mu shige mu duba da kan mu”. Rigima ce ta barke tsakanin samarin da Inna Hure, ta kasa ta tsare ba wanda zai shiga, suna tsaka da rigima uban yaron ya bangaje Inna Hure ya shige gidan suma sauran matasan suka shigo, kaf sun duba ko'ina amma babu Nafi babu dalilinta. Nan fa suka fara masifa suna faɗin an san inda aka ɓoye ta, inna hure ba haƙuri ta biye musu. Kamar abun arziƙi duka suka fice daga gidan. Inna Hure ta ci gaba da masifa faɗi take yi, Yau sai Nafi ta bar mata gidanta. https://hikaya.bakandamiya.com/zuciya-1/
👍 ❤️ 3

Comments