Hikaya
Hikaya
February 8, 2025 at 07:55 AM
Rayuwata 1 | Bakandamiya Hikaya Takan dimaucewa tare da kara azama aduk lokacin data ji dajin yayi amsa kuwwar amon tashin bindiga, wanda takeji kamar a cikin kwakwalwarta ake halba war, a duk sa’adda taji tashin bindigar tanaji ne kamar itama tata kwakwalwar akeson fiddawa daga cikin kanta kamar yanda taga an yiwa wasu mutane da kuma wasu daga cikin yan uwanta ace cikin kauyen nasu data baro,  tashin hankali tare da tsoro sukan kara mamaye illahirin zuciyarta wanda hakan kan kara mata dauriya tare da juriya hade da jajircema wahalar gudun da take faman yi,a iya nata tunanin da hangen ta hakanne kawai hanyar tsira idan tayi kokarin tserema yan bindigar da keta faman halbin kan uwa da wabi. https://hikaya.bakandamiya.com/rayuwata-1/
👍 ❤️ 3

Comments