Hikaya
February 10, 2025 at 12:56 PM
So Da Buri 1 | Bakandamiya Hikaya
Umma ce ta ce "wato da ka d’auka ba yanzu zan dawo ba ko? Shi ne kaje harda wani d’ago ta kana kallon ta, idan za ta had’iyi zuciya ta mutu Junaidu ina ruwanka da damuwarta?? Ka ga ta inda Ja’afar ya fi ka ko? Yaron nan ko kyalle ne indai nace banaso to kuwa shima ba zai so shi ba, anya ni na haifeka kuwa?A ce Yaro kwata kwata baya kishin uwarsa!! An bi an lashe ka an shanye ka to wallahi ba’a isa ba, ni naci uwar boka ma ballantana malam. Ka ci gaba da b’ata mini rai har sai ka ja nai maka baki tunda baka jin magana ta duk da dai na san ba yin kanka ba ne ba.”
https://hikaya.bakandamiya.com/so-da-buri-1/
👍
❤️
4