Hikaya
Hikaya
February 10, 2025 at 01:11 PM
Zinariya 2 | Bakandamiya Hikaya Gudun da lokaci ke yi baya hana rayuwa da abunda rayuwa ta ƙunsa tafiyar da al'amurransu, tsawon shekaru ashirin da biyar kenan da haihuwa Zinariya, in da ƙaddara ta zaɓar ma Zinariya zama a duniyar jinnu wanda ba lallai hakan ya zame mata abu mai sauƙi ba. Cikin shekarun nan Zinariya ta rayu ne har ta kawo yanzu cikin tsanani da wahala dan rayuwa na yi mata Matuƙar wahala a ƙarƙashin inuwar waɗanda ba jinsinta ba. Zaune take akan wani dutsi mai matuƙar girma da faɗi, an ƙawata dutsin da magudanar ruwa da kuma furanni da aka killace a duk wata kwana da za a iya tsugunnawa ko a zauna, lilo take yi da ƙafafunta tayi shiru da alama ta zurfafa cikin tunani. Wata Ƙatuwar mage ta bayyana gabanta, a ɗan razane ta ja baya jin magen gefenta, ta zuba mata ido tana sauke ajiyar zuciya. Magen ta matse jikinta sosai nan take jikinta ya rikiɗa zuwa bil'adama. https://hikaya.bakandamiya.com/zin
👍 ❤️ 6

Comments