
Hikaya
February 12, 2025 at 08:14 PM
Mutuwar Tsaye 40 | Bakandamiya Hikaya
Juyawa ya yi wurin ɗayan da shi kuma a kan matarsa da ya saka ne, "Matarka aure zata yi, kuma zata haihu, sannan mutuwa ce zata raba ta da mijinta, don haka ka je ka saurari Allah kawai."
Ko kusa bai ji daɗin hakan ba, cewa ya yi "Ba wata mafita?", Malamin ya ce "Akwai, ita da makaho duk mataki ɗaya za a ɗaukar musu, ba za a bari su zauna lafiya ba.."
Wasu laƙunƙuna da layu ya basu, su kuma suka jibga mashi kuɗaɗe, sannan suka tafi.
Uwa mai daɗi! A lokacin da Dr. Bello ke ƙulla ma Deeni makirci, a lokacin ne ta zage dantse wurin yi ma ɗanta addu'a da kuma halsataccen magani, ta san akwai makircin mutane sosai a cikin halin da Deeni ya samu kansa, don ko ba asiri, toh akwai kambun baka, saboda kusan sunan Deeni ya zagaye ko'ina acikin garinsu, har ma da wasu garuruwan.
Lokuta da dama an sha yi mata tayin Malamai ƴan tsubbu wurin nema ma Deeni magani, amma bata taɓa yadda da batun ba, saboda gudun rasa imani da kuma dukiya, sai dai duk inda ta ji Malaman Islamic tana aikawa, wani lokaci har gida suke iske Deeni saboda karamci, kuma suna ƙoƙarinsu wurin bashi addu'oi masu kyau, shi ya sa ƙullinsu Dr Bello bai hana tauraruwa Deeni haskawa ba, don har gida yanzu iske shi ake akan aikinsa.
https://hikaya.bakandamiya.com/mutuwar-tsaye-40/
👍
❤️
3