Hikaya
Hikaya
February 14, 2025 at 08:55 AM
Tsakaninmu 1 | Bakandamiya Hikaya Duka mai rai mamaci ne, amman kuma yawo kakeyi da sanin cewa ajali zai iya riskarka kowanne lokaci, a wajen mace mai ciki kamar abin ya bambanta, rayuwa take a cikin wata duniya ta taradaddi, kamar cikin na tare da wani tikiti ne na karewar rayuwa ko akasin hakan, gareta da abinda take dauke dashi, duka wata taran nan da wahalar, nakuda na iya riskarta ta haihu, dan ya koma, ko ita ta tafi ta barshi. Sosai Sa'adatu a yau take ganin babu wanda ya kai mace mai ciki mika dukkan lamurranta a hannun Allaah, shisa ma har take da sukunin gudanar da al'amuran yau da kullum batare da tunani da firgici sun kassarata ba. Saita tsinci kanta da yiwa Fa'iza sannu tana sakata yin dariya. Haka ta kwanta ranar ma tana rasa zaren da zata kama ta kulla a matsayin tunani, da kiran Aisha ya shigo wayarta kuwa bugun da zuciyarta tayi da bata da wadatacciyar lafiya tabbasa saita samu matsala, ba iya kiran kawai ta kashe ba, gabaki daya wayar ta kashe. Sai bugun zuciyarta ya zama wani sauti daya hana mata bacci, idan ta rufe idanuwanta sai taji kamar ya karu, wayarta a kashe yake, ta gane baccin bai fara daukarta ba sai gab da asuba, saboda yanda akayi kiran sallar farko akan kunnenta, dakyar taja kafa ta fita tayi alwala. Akan dardumar data idar da sallah ta kwanta, bacci mai nauyin gaske ne ya dauketa, shisa ta dauka a mafarki take jin muryar Abdallah yana tashinta "Fa'iza nakuda takeyi Sa'adatu, kizo ki zauna da ita in samo abin hawa mu tafi asibiti..." https://hikaya.bakandamiya.com/tsakaninmu-1/
👍 ❤️ 7

Comments