
Hikaya
February 14, 2025 at 09:03 AM
Shirin Allah 1 | Bakandamiya Hikaya
Jin ya sake ta yasa ta bude ido tana kallon kofar. Wani matashin saurayi ne tsaye ya harɗe hannayensa yana duban su waige -wangen inda za ta ga gyalenta ta kama yi takalmanta ta fara gani ta wawuro su kafin ta ga gyalen ta hada da shi ta nufo kofa matashin ya ba ta hanya duk abin nan kuma kuka take tana fita ya mara mata baya yana duban yadda take tafiya tana kuka sai da ta yi nisa ta tsaya ta sanya takalmi da gyalen tsirarun ma'aikatan da ke bin ta da kallo ba ta ko san suna yi ba.
Maimakon shago gida ta wuce ƙwanƙwasa get din ta yi ta yi duk da ba ta da yaƙinin akwai mutum, sai kuma ta ji takun tafiya an zo an buɗe , Malam Buhari ne wanda shigowar sa kenan daga wurin aiki, ganin ta a birkice yasa ya tambaye ta abin da ya same ta ta ce ba komai, ciki ta wuce ta haye saman katifarsu tana kuka tana kullawa da kwancewa yadda za ta koma Daura.
Muryar Gwoggo Indo da ta ji ba ta sanya ta ɗaga kai ba har ta dafa kafaɗarta "Me zai sanya ki yi mini haka Hamida? Me ya faru kika taho ban sani ba? Shiru ba ta ba da amsa ba tsawa ta kwatsa mata "Tashi zaune mu yi magana! Ba shiri ta tashi don ko banza ba ta taɓa yi mata tsawar ba "Na ce "Me ya same ki? Ta fada cikin zare ido cikin inda inda ta bata labarin sama sama. Wayarta da ke hannunta ta shiga latsawa "Sannu tsohon banza mai kokarin ɓata ƴaƴan jama'a." abin da ta fara cewa kenan tana huci, da alama shi ma tsiyar ya tarbe ta da ita. "E ko da nake kwaɗayayya ban zama fasiƙa ba, ka gode wa Allah da ya ce ce ka ba ka ɓata mini yarinya ba, da Kano sai ta yi maka kaɗan."
A takaice dai tsiya suka kwasa ta sauke wayar tana ci gaba da masifa, bala'inta ya shigo da Malam Buhari yana tambayar abin da ya faru ba ta saurara ba da ƙyar ya lallashe ta suka bar falon.
Tun daga ranar Hamida ba ta kuma yarda ta je kai abinci kowanne Office ba.
https://hikaya.bakandamiya.com/shirin-allah-1/
👍
❤️
😂
6