Hikaya
February 18, 2025 at 05:59 AM
ABUBUWA GUDA BIYAR DA ZA KU IYA AMFANA DA SU IDAN KU KA ƊORA AIYUKANKU A MANHAJAR BAKANDAMIYA HIKAYA
Hikaya manhaja ce da aka samar da ita domin marubuta da kuma masu karatu. Akwai litattafai masu tarin yawa da masu karatu za su iya zaɓar wanda ya yi musu su karanta, ko dai a kyauta ko kuma a wani ɗan farashi mai rahusa. Baya ga wannan, akwai kuma muƙaloli ta tattaunawa da aka yi da marubuta da masu sha'awa za su iya shiga su karanta domin su ƙaru. To amma a matsayinka/ki na marubuci/marubuciya ko akwai wani abu da za ku amfana da shi yayin da ku ka ɗora aiyukanku a manhajar? Tabbas akwai! Ga kaɗan daga cikinsu;
1. Abu na farko da za ku amfana da shi, shi ne samun talla cikin sauƙi. Burin kowane marubuci shi ne rubutunsa ya yi tafiya mai nisa kuma mutane masu tarin yawa su karanta abinda ya rubuta. Idan ku ka ɗora aiyukanku a Bakandamiya Hikaya to dukkan masu bibiyar taskar, waɗanda Allah ne kaɗai Ya san iya yawansu daga ko'ina suke a faɗin duniya za su gani sannan ku ma kuna iya yi wa naku mutanen sharing na link domin su ma su gani. Kuma wannan garaɓasar tana ga masu ɗora aiyukansu don samun kuɗi da kuma masu ɗorawa a kyauta gaba ɗaya.
2. Garaɓasa ta biyu kuma ga waɗanda ke ɗora aiyukansu a Bakandamiya Hikaya ita ce, ba ka buƙatar sai ka sha wahalar yin bangon littafi, mu za mu yi maka da kanmu. Ko da yake kana iya turo da naka idan kana so, amma namun sau da dama ya fi.
3. Kuna iya samun kuɗi masu tsoka idan littafin ku ya cika ƙa'idoji da sharuɗɗan da aka gindaya. Wannan batu kuwa sahihi ne domin mutane da dama sun yi hakan kuma sun tabbatar.
4. Ko da kun ɗora aikinku a bisa kyauta ne ko kuma na kuɗi, haƙƙin mallakar aikin dai na nan a hannunku, kuma duk inda labarin zai je da sunanku zai tafi.
5. A wannan zamani da muke ciki na ci gaba da aka samu na na'urar zamani, Hikaya ce kaɗai sahihin wurin da za ku ɗora aiyukanku hankali kwance ba tare da fargabar komai ba.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin irin abubuwan da za ku amfana da su yayin da ku ka ɗora aiyukanku a shafin Bakandamiya Hikaya.
Ya ku 'yan uwan marubuta, tsoffi da sabbi, Hikaya na maraba da ku da aiyukanku a ko'ina kuke a cikin faɗin duniya, kada ku bari wannan dama ta wuce ku, ku ba da dama duniya ta ƙaru da fikira da basirarku ta hanyar ɗora aiyukanku a shafin Hikaya.
Domin shiga shafin sai ku shiga wannan adireshin 👇👇👇
hikaya.bakandamiya.com
Ko kuma ku sauke manhajar daga Playstore
👇👇👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.bakandamiya.hikaya
Domin neman ƙarin bayani sai ku tuntuɓi wannan lamba ta WhatsApp: 09072304745
ko kuma ta adireshin email: [email protected]
Hikaya, shafin marubuta da masu karatu domin marubuta da masu karatu.
👍
❤️
😮
5