Hikaya
Hikaya
February 20, 2025 at 06:03 AM
Mijin Novel 8 | Bakandamiya Hikaya Har dariya take ba Hindun, sai dai duk baudadden halinta tana da dadin zama, saboda tana da wani irin kirki da ba ko yaushe ake samun mutane masu irin shi ba yanzun, sai dai tana cikin mutanen da ake kira 'kai fi daya' kuma cikin wanda ake cewa su 'tsaye' suke, shisa sai kayi tunanin magana Dimples ta fada maka wasu lokuttan, amman har ranta hakikanin gaskiyarta ta fadi, bata damu da ya zaka dauki hakan ba. Shisa suke fada da Hindu wasu lokuttan, saboda tana mata fadan gaskiya. Hindu ta saka a key zata ajiye sai taji 'dit' alamar sako ya shigo, da sauri ta danna ta cire key din ganin notification din na Instagram ne, shiga tayi tana budewa, zuciyarta na wani irin tsalle ta dawo wuyanta, kafin ta koma kirjinta tana cigaba da dokawa kamar zata fito, ganin da tayi Hamza ne ya amsa sallamarta, ya dan dauki mintina kafin taga ya turo hoton da tayi saurin budewa tana ganin 'Rough sketch' daya warware matsalar da ta kasa na zanen nata, sai dogon sharhi cikin gamsashen bayani daga kasa. Wani irin murmushine ya subuce mata, tayi wani tsalle tana dawowa kan gadon, hadi da mirginawa tana jin kamar an mata albishir da kujerar hajji da duk wani cikar burinta saboda farin cikin daya lullubeta, tuntuni inda tasan maganar Architecture itace zata saka Hamza ya kulata a DM da tafi shekara da tura mishi, yanda in tayi mishi a comment section yake yin biris da ita yasa bata taba tunanin zai amsa mata magana ta private ba. Hamza fa, Hamza Abu Abbas ne ya zauna yayi mata bayani harda zane yanda zata fahimta sosai. Rubutu ta soma yi tana tura mishi https://hikaya.bakandamiya.com/mijin-novel-8/
👍 ❤️ 🙏 5

Comments