Hikaya
Hikaya
February 20, 2025 at 06:07 AM
Uwata Ce Sila 2 | Bakandamiya Hikaya "Zainab in kin isa ki zo ki sani in daina cewa UWATA CE SILA an ma daina ce miki Anty kuma wallahi tun da dai hakane yau zan tona, kuma kema kanki har da saka hannun ki kuma wallahi da ke da Mom ba zan ta'ba ya fe muku ba kun cuce ni kun zalumceni." ta rushe da kuka tayi cikin d'akin ta tana kuka. Duk abin da Ameera ta ce Mom tana ji kuma ta na so ta sa maganar a mizanin kanta domin ta auna amma ina ta kasa, amma kuma tin da de ta ce zata fad'a tom shi kenan ita ma dama Mom d'in haka ta keso. Take kuwa ta ciro waya ta shiga kiran Uncle Bala d'in, sannan tabi bayan Ameera d'akin ta. Kuka take yi babu ƙaƙƙautawa Mom ta zo ta same ta "Ameera" Mom d'in ta kira sunan ta amma bata amsa ba ba ta ma nuna ta san da shigowar taba "Ameera" ta sake kiran sunan ta a karo na biyu, cikin masifar da ta sama ji daga bakin d'iyar tata yau ma ta fara "Ki fi ta min daga d'aki wallahi bana son ganin ki in ba haka ba zan kashe kaina kowa ya huta, Kifita naceeee!!" Ta 'karasa maganar cikin wani mahaukacin tsawa kai ka ce tana magana da yar cikin tane ba mahaifiyarta ba. https://hikaya.bakandamiya.com/uwata-ce-sila-2/
👍 ❤️ 😮 🙏 7

Comments