
Hikaya
February 20, 2025 at 07:17 AM
Addininmu 3 | Bakandamiya Hikaya
Fitowa da kud'in tayi ta girga taga dubu d'ari harda tara, aikuwa ta bud'e baki da hanci tana mamaki me yasa ta d'ebo da yawa, take ta saka a cikin jakar school d'in ta, sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa gamida sau'ke abun da ta tara a cikin ta tsabar far gaba. Riga da wando ta saka na Adidas sannan ta nufi kiching domin samun abun da zata ci, tana shiga tayi karo da Mommy a ciki tana had'a musu abincin yamma.
Cike da mamaki Mommy take kallon ta, cikin yaran su Mommy ta ce "Daga ina kike?
"Mommy nadawo tin d'azu zan shiga gida naga kun rufe gidan shine na koma sai yanzu nadawo. Mommy ta bud'e baki zatayi magana taji muryar Samuel a d'akin Daddy yana ihuu ai kuwa suka nufi gurin da gudu. Cikin fushi Daddy ya ke cewa "I see wer is my money? Samuel na kuka yana cewa "Daddy banine na d'auka ba Allah nima yanzu na shigo.
https://hikaya.bakandamiya.com/addininmu-3/
👍
❤️
😮
🙏
8