Hikaya
Hikaya
February 24, 2025 at 01:58 PM
Mutum Da Kaddararsa 60 | Bakandamiya Hikaya "Akan me ita matar ta shi fa? Na taɓe baki Ni ya kalallame ya ce in riƙa mishi." Suka dubi juna Hafsa ta ce "Ikon Allah idan ba ka mutu ba za ka ga abu, dama ana haka gaskiya ki canza taku Bilkisu, ya za a yi ya mayar da ke kamar wata shashasha ta kwana da miji ki yi musu girki? Amma fa ki yi haƙuri ba zuga ki nake ki bijire wa mijinki ba mu ma nan duk muna da mazajen kowacce da ƙalubalen da take fuskanta a ta ta rayuwar auren. Amma dai wannan ita ma ta fito ta yi ki yi shi kenan idan ma ba za a bari ki yi arba'in ɗin ba. Khadija da ta rafsa tagumi ta ce "Allah ji nake har zuciyata na tafasa wannan wane irin rashin yanci ne ita ce mai yanci ta ƙi yin girki ta kwana da miji mai jego da shiga kitchen ta yi ƙwafa ku raba kawai ta yi na ta ki yi naki shi kenan. Ni kin ga ma budurwa ce a waje ba ma a aure ta ta shigo ba amma ta zama kamar kishiyata kuma hakanan nake hakuri ya za ka yi lamarin nan na maza. Duk suka gama zantukan su ina sauraren su na kuma dauki shawarwarin su tsaf. https://hikaya.bakandamiya.com/mutum-da-kaddararsa-60/
👍 ❤️ 5

Comments