Hikaya
Hikaya
February 24, 2025 at 07:21 PM
Su Ne Sila 11 | Bakandamiya Hikaya D.S.P ya dube ta ya na faɗin "Doctor zai iya yuwa garau take ji kawai kissa ne irin na ta tunda ta san daga nan ina za ta tafi dole ne za ta yi duk abin da za ta yi dan ɓangarar da tunanin mu domin yin hakan ya ba ta damar aikata wani abun" murmushi Dr Hafiz ya yi kafin ya ce "ba na tunanin za ta yi wani abun ku dai ƙara haƙuri idan an yi dukan auni-auni an tabbatar da lafiyarta sai a ba ku sallama ku tafi da ita ɗin". "Am..." Hannu Dr Hafiz ya ɗaga masa yana faɗin "ka yi haƙuri D.S.P a yi yadda na ce ba kuna tare da ita ba, 'yansada uku ne a ƙofar ɗakin nan bayan kai cikon na huɗu ga shi duk da ba ta da lafiya kun ɗaure ta to duk ta ina za ta samu ta tsere ma ku". https://hikaya.bakandamiya.com/su-ne-sila-11/
👍 ❤️ 5

Comments