Hikaya
February 24, 2025 at 08:32 PM
Zarge 8 | Bakandamiya Hikaya
Hannunsa ya goya a bayansa, zuciyarsa na masa ba daɗi. Domin har kawo yanzu ji yake hankalinsa bai kwanta ba game da lamarin budurwar Umar. Ga shi ba shi da contact nata ballantana ya ƙitaya ya ji wani hali take ciki.
A hankali ya shafa wuyansa yana haɗiyar wani abu a maƙoshinsa, wanda ya sa Adam's Apple ɗinsa ya motsa sama da ƙasa. Kujera ya dafa, sannan ya zauna a kan kujerar yana furzar da huci kaɗan, duk ya rasa me ya kamata ya yi. Wani abu ya tuna, dan haka ya ɗauki wayarsa, sannan ya lalubo lambar Umar ya aika masa da ƙira.
https://hikaya.bakandamiya.com/zarge-8/
👍
❤️
🥰
5