
Hikaya
March 1, 2025 at 10:55 PM
Mutuwar Tsaye 44 | Bakandamiya Hikaya
Buƙatunsu suka cigaba da faɗa ma Ubangiji, sai da suka ga cunkoso ya rage ne suka tashi, wurin Asma'u Bashir ya je suka dawo tare wurinsu Deeni, ɗawafi suka shiga yi, haɗe da ambaton Allah. Deeni kuwa burinsa shi ne ya ji sa a jikin Ka'aba, a hankali yana zagayen ta, yana kuma ƙara shige mata, cikin ikon Allah kuwa sai gashi ga ta. Ya Salam, bai san lokacin da ya fashe da kukan godiyar Allah ba, dafa ta ya yi haɗe da kifa kansa a jikinta, zuciyarsa ba zata iya misalta irin nutsuwar da ta samu ba, domin ta linka irin nutsuwar da ɗa ke ji idan yana rungume a jikin mahaifiyarsa, sannan ta linka irin nutsuwar da masoyi ke ji idan ya ji sa a jikin masoyinsa. Kawai dai sai wanda ya samu kansa a wannan yanayi ne zai iya describe na abin da ya ji.
Uban tafiyar kuwa farincikinsa shi ne na zuwa wurin da bawa bai zuwa da buƙatunsa face an karɓa mashi. Sallar Asham suka gabatar tare da sauran jama'a, bayan an gama ne suka yi adduo'in godiya ga Ubangiji Allah. Deeni ne ya kasa haƙuri, duban Bashir da Lalu da suka sanya shi a tsakiya ya yi "Kun san me?", suka ce "A'a", idanunsa na kallon ɗakin Allah ya ce "Tabbas duk wanda ke da damuwa idan ya zo nan, toh damuwarsa ta ƙare", Tambayar shi Lalu ya yi "Me yasa ka ce haka?", saboda komai na da dalili, Deeni ya ce "Idanuna nake jin kamar ban taɓa ciwon ido ba, tar nake ganin komai a masallacin nan", Bashir ya ce "Masha Allah, ai ka'aba ta wuce duk tunanin mai tunani a wurin girma da mu'ujiza", Lalu da ke cikin nutsuwar zuciya ya ce "Gaskiya ne, Allah ya sa mun shigo a sa'a", suka ce "Amiiiin ya Allah."
https://hikaya.bakandamiya.com/mutuwar-tsaye-44/
❤️
2