
ZAURAN DALIBAN ILIMI
May 28, 2025 at 09:37 PM
Menene a ka hana wanda yake da niyyan yin layya aikatawa? shin kuma hanin ya shafi sauran iyalanshi?
Daga Ummu Salamah RA, cewa Manzon Allah ﷺ yace:" Idan kuka ga jinjirin watan Zhul hijjah kuma ɗayanku yana da nufin yayi layya, to ya kame daga aske gashinsa da kuma yanke ƙumbarsa. Muslim
A wata riwayar: "Kar da ya cire gashinsa ko wani abu na fatan jikinsa.
Shaykh Muh'd Saleh Al'Uthaimeen ya ce: "Wannan hukuncin ya keɓanci wanda zai yi layyan ne, amma wanda yi mishi layyan za a yi to ba shi da alaƙa da wannan, domin Manzon Allah SAW cewa yayi: "Kuma ɗayanku yayi nufin yin layya.." bai ce: ko za a yi mishi layya ba, kuma saboda Manzon Allah SAW ya kasance yana yin layya wa iyalansa amma ba a naƙalto cewa ya umarcesu daga kamewa daga wannan ba(yanke ƙumba/farce ko fitar da gashi).
#zaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi
INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24