
ZAURAN DALIBAN ILIMI
2.5K subscribers
About ZAURAN DALIBAN ILIMI
Ƴan uwa masu albarka ku yaɗa alkhairi, ku yaɗa ilimi ga al'umma za ku samu ladaddaki masu yawa, Manzon Allah ﷺ ya ce "Wanda yayi nuni a kan wani alkhari yana da ladan wanda ya aikatashi". Muslim Ibnul Mubarak(RA) ya ce: Babu wata daraja mafi falala da ɗaukaka bayan Annabta kamar yaɗa ilimi mai amfani. Ku zuba hannayen jarinku ta hanyar yaɗa ilimin Addini barakallahu feekum💌 TELEGRAM https://t.me/Zaurandalibanilimi IG https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24 FB https://www.facebook.com/Zaurandalibanilimi
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

KYAUTATA MU'AMALA GA MUTANE Al-hafiz Ibn Rajab (Rh) ya ce:- Sau da yawa mu'amalantar mutane da magana mai dadi ya fi soyuwa a garesu daga ciyar da su abinci ko kyautata musu ta hanyar ba su kyautan kudi, Kamar yanda Luqmanul hakeem ya fada wa dansa cewa: Yaa kai 'dana: Ya kasance maganarka ta zamto mai dadi, kuma ka zamto mai sakin fuska ga mutane, za ka zama mafi soyuwa a gurin mutane fiye da wanda yake ba su dinari da dirhami. ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﺮﺳﺎﺋﻞ : ١٠٠/ ١ #Zaurandalibanilimi TELEGRAM https://t.me/Zaurandalibanilimi WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

FALALAR GOMAN FARKO NA ZUL HIJJAH Manzon Allah SAW yace: "Babu wasu kwanaki da ayyukan ɗa'a a cikinsu suka fi soyuwa ga Allah kamar waɗannan kwanakin- yana nufin goman farko na Zhul Hijjah, suka ce yaa Manzon Allah har da Jihadi saboda Allah, yace: har da Jihadi saboda Allah, sai mutumin da ya fita da kanshi da dukiyarsa sannan bai dawo da komai ba". Bukhary #Zaurandalibanilimi TELEGRAM: https://t.me/Zaurandalibanilimi WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

Menene a ka hana wanda yake da niyyan yin layya aikatawa? shin kuma hanin ya shafi sauran iyalanshi? Daga Ummu Salamah RA, cewa Manzon Allah ﷺ yace:" Idan kuka ga jinjirin watan Zhul hijjah kuma ɗayanku yana da nufin yayi layya, to ya kame daga aske gashinsa da kuma yanke ƙumbarsa. Muslim A wata riwayar: "Kar da ya cire gashinsa ko wani abu na fatan jikinsa. Shaykh Muh'd Saleh Al'Uthaimeen ya ce: "Wannan hukuncin ya keɓanci wanda zai yi layyan ne, amma wanda yi mishi layyan za a yi to ba shi da alaƙa da wannan, domin Manzon Allah SAW cewa yayi: "Kuma ɗayanku yayi nufin yin layya.." bai ce: ko za a yi mishi layya ba, kuma saboda Manzon Allah SAW ya kasance yana yin layya wa iyalansa amma ba a naƙalto cewa ya umarcesu daga kamewa daga wannan ba(yanke ƙumba/farce ko fitar da gashi). #Zaurandalibanilimi TELEGRAM https://t.me/Zaurandalibanilimi INSTAGRAM https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

KWANAKI GOMAN DHUL HIJJAH Shaykh Ibnul Uthaimeen(RA) ya ce: "Abun mamaki mutane suna gafala da wadannan kwanaki goman(Na Dhul hijjah)! sai ka samesu a goman karshe na ramadan su na dagewa gurin aiki, amma a goman Dhul hijjah da kyar ka samu wani ya banbanta ta(goman Dhul hijjah) da kwanakin da ba su ba(ta hanyar yawaita ayyukan da'a a cikinsu sama da sauran kwanaki), kuma da mutum zai tashi ya yi aiki na kwarai a wadannan kwanaki goman don ya raya abin da Manzon Allah(SAW) ya yi nuni da shi na ayyukan kwarai, (to in ya yi hakan) lallai shi ya na kan alkhairi mai girma". #Zaurandalibanilimi TELEGRAM https://t.me/Zaurandalibanilimi INSTAGRAM https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24