
ZAURAN DALIBAN ILIMI
May 28, 2025 at 09:38 PM
AZUMTAN KWANAKI GOMA(10) NA ZUL HIJJAH BAN DA RANAR IDI
Shaykh Muh'd Saleh Al'Uthaimeen RA yace:" Azumtar Goman Zul hijjah ban da ranar Idi wannan babu shakka yana daga cikin ayyuka nagari. Domin Manzon Allah SAW yace:"
Manzon Allah SAW yace: "Babu wasu kwanaki da ayyuka nagari a cikinsu suka fi soyuwa ga Allah kamar waɗannan kwanaki Goman, suka ce yaa Manzon Allah har da Jihadi saboda Allah, ya ce: har da Jihadi saboda Allah, sai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa sannan bai dawo da komai ba".
Saheeh Attirmidhi 757
Sai Azumi ya kasance a karkashin umumin wannan hadisin.
(لقاء الباب المفتوح، صوم التطوع).
#zaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi
WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N
