
ZAURAN DALIBAN ILIMI
June 4, 2025 at 08:59 AM
YIN LAYYA DA DABBA MAI TSADA NE YA FI FALALA KO DABBA MAI GIRMA?
Shaykh Muh'd Ibn Al-Uthaimeen(RA) ya ce: "Idan mu ka yi dubi ga amfanin abin layya babba mai nama da yawa ta fi, Amma idan mu ka yi dubi ga gaskiyar bauta ga Allah Madaukaki sai mu ce mai tsada ta fi falala.
Sai dai amma kai ka duba ka ga wanne ne ya fi gyara da inganta zuciyanka sai ka yi shi, idan ka ga zuciyarka imaninta yana karuwa haka tana kara kaskanta ga Allah idan ka fitar da kudin mai tsadan to ka bayar din".
مجموع الفتاوى 35/25
#zaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi
WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N
