ZAURAN DALIBAN ILIMI
ZAURAN DALIBAN ILIMI
June 5, 2025 at 06:51 PM
*SUNNAH NE FITAR MATA ZUWA IDI* An ruwaito daga Umm Ad'iyyah(RA) ta ce: Manzon Allah ﷺ ya umarce mu a sallah karama da sallah babba da mu fitar da yantattun yan mata da masu aure, da tsofaffi, amma ya umarci masu haila da su nisanta daga gurin sallar musulmai". A wani lafazin: "Mun kasance a na umartanmu da fita a ranar Idi, har muna fitar da budurwa daga dakinta, har mu fitar da mai haila, sai su kasance a bayan mutane, su rinka yin Kabbara da Kabbarorinsu, su rika yin addu'a da addu'oinsu, suna fatan samun albarkan wannan rana da tsarkinta". Muttafaqun alaihi Mata za su fitane sun suturce jikinsu da hijabi ingantacce, ban da fitar da ado da tsaraici, kuma ban da sanya turare. #zaurandalibanilimi TELEGRAM https://t.me/Zaurandalibanilimi WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N
Image from ZAURAN DALIBAN ILIMI: *SUNNAH NE FITAR MATA ZUWA IDI*  An ruwaito daga Umm Ad'iyyah(RA) ta c...
🙏 ❤️ 😂 5

Comments