Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 9, 2025 at 04:25 PM
Barinmu kowace mace ta yi aure, domin duka mata ƴan'adam ne, babu wadda ta rako mata duniya. Yawan adadin mata sama da maza (surplus of women) matsala ce da kusan kowace ƙasa ta duniya take fuskanta a yau. Alhamdu lilLah da ni'imar musulunci, domin shi ne addinin da ya magance wannan matsalar, ta hanyar halattawa maza auren mace fiye da ɗaya har zuwa huɗu. Idan muka duba al'ummarmu, akwai mata dayawa, ƴan mata da zawarawa, suna son aure, domin suma mutane ne kamar kowa, suna da buƙata koda ba su faɗa ba, don haka dole ne mu ƙarfafa gwuiwar maza masu hali da su ƙara aure, domin raya sunnar Annabi ﷺ da warware matsalar al'umma. Su kuma matan da suke daga ciki su yi haƙuri, duk da cewa rauni da kuma son rai ba zai bari su gamsu da maslahar ƙarin aure ba. Kowace mace tana son ƴan'uwanta su yi aure, ƴaƴanta mata su yi aure koda a matsayin kishiyar wata ne, amma ba ta son mijinta ya auri wata. Babu wani wa'azi a duniyar nan da zai gamsar da mata su karɓi kishiya, kuma fa dukkansu mata ne, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne! A yayin da muke kira da maza masu hali da su ƙara aure, muna kiransu da su riƙa kamanta adalci da kuma halacci, kada su manta da alherin baya. Amma kada wani alherin uwargida ko kyautatawarta ko kirkinta ya hana ka yi mata kishiya, haka nan kada barazana ko tausayi ya hana ka yi mata kishiya. Ka sanya a ranka ƙarin aure haƙƙinka ne, ba ka yi wa kowa laifi ba don ka ƙara aure, kai dai ka yi adalci, sa'an nan a lallaɓa uwargida, a yi mata kyaututtuka na dannin ƙirji. - Isa Sadi
👍 ❤️ 🙏 😠 😢 🥰 16

Comments