
Sirrin rike miji
June 9, 2025 at 04:33 PM
HALAYYAR DANKA ** MADUBIN HALAYYARKA NE
■ Danka ya cika karya da yawa ** Ma’ana kana tsananin bin diddiginsa.
■ Danka ba shi da karfin zuciya ** Ma’ana ba ka karfafa masa gwiwa.
■ Danka bai iya magana ba ** Ma’ana ba ka yin hira da shi.
■ Danka yana sata ** Ma’ana ba ka koya masa yin kyauta ba.
■ Danka matsoraci ne ** Ma’ana kana yawan kare shi.
■ Danka ba ya ganin girman mutane ** Ma’ana kana yawan daka masa tsawa.
■ Danka kullum cikin fushi ** Ma’ana ba ka yabonsa.
■ Danka marowaci ne ** Ma’ana ba ka sanya shi cikin al’amuranka.
■ Danka yana cin zalin mutane ** Ma’ana kai mai kaushin hali ne.
■ Danka yana da rauni ** Ma’ana kana yawan yi masa barazana.
■ Danka ya cika kishi ** Ma’ana ba ka kula da shi.
■ Danka yana yawan damunka ** Ma’ana baka rungumarsa ka sunbance shi.
■ Danka ba ya yi maka biyayya ** Ma’ana ka cika yawan ba da umarni.
■ Danka ba ya shinga mutane ** Ma’ana ka shagalta da yawa.
~~ In ji: Dr. DARIK AL HABIB
👍
🙏
🤔
😮
12