Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 10, 2025 at 06:02 AM
Miji kan ji kin RENA shi in ........................ ●Ya na magana kina magana ●Ya sa ki abu ki ƙi yi ●Ya hana ki abu ki yi ●Ƙin amsa kiran sa a shimfiɗa ●Nuna masa tamkar alfarma kike masa a shimfiða ●Fada masa baƙaƙen maganganu ●Yi masa magana kamar da yaro kike magana ●Rena abunda yake miki ●Nuna gazawar sa wajen riqe ki ●Wulaqanta abunda ya miki ko ya kawo ●Kwatanta shi da wani ( dan uwan sa, aboki, abokin aiki ko makwabci) ●Kwatanta abunda yake yi a gidan sa da abunda wani yake ma gidan sa ●Masa tirjiya, musu ko rashin kunya ●Yi masa titsiye kamar yaro ko sa'an ki ●Wulaqanta shi, 'yan uwan sa ko abokan sa ●Ki masa laifi ki ƙi bashi hakuri ●Ki masa laifi ki ƙi yarda da laifin ko ki bada hujjan dayasa kike ganin ba laifi bane ko shiyasa kikayi abunda kikayi ●Kiyi abu ba tare da sanar dashi ba kamar fita ●Mu'amalanta ko zuwa inda baya son kije ko hulda da su ●Taɓa masa ko Amfani da abun sa ba da izinin sa ba ●Kai maganar sa ko matsalolin ku inda bai dace ki kai ba ●Gorin abunda kika masa ko iyayen ki su masa ●Qaskantar da samun sa, sana'ar sa ko aikin sa. ● Bibiya rayuwa da masa bincike ● Gindaya masa sharuɗa kamar yaro ●Etc Wadannan abubuwa na daga cikin abunda ke sa miji yaji kin rena shi, matuqar kina son zaman lafiya dashi dole ki kiyaye aikata su ko furta su. ✍️ Fatimah Chikaire
🙏 👍 😮 10

Comments