Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 10, 2025 at 08:11 AM
akwai wasu yammata da sukayi aure kuma an dade da su anan Facebook ana zumunchi shaukin dadin aure da soyayyar mijinsu da kuma farin cikin sunyi eid lafiya da mazajensu wannan farin cikin yasa sun kasa boyewa har saida sukayi hoto da mazajensu cikin kwalliyar sallah suka daura anan Facebook duk da ina lura dasu sunyi kokari sosai wajen rufe kansu harma da mazajen nasu wasu sun saka iya hoton kafafuwa wasu kuma iya hoton hannaye yadda mutane suka sako su a gaba wasu daga cikinsu akwai alamin depression ma zai iya kamasu sakamakon bad comments daga mutanenmu na Facebook duk da wasu sunyi musu fatan alkhairi wasu sun sa musu albarka abun da ya kamata su fahimta shine Facebook wata irin murdaddiyar duniya ce data hada mutane kala daban daban wasu masu fatan alkhairi wasu masu fatan sharri wasu mutanen suna da negativity komai a bahagon ce suke ganinsa wasu kuma suna da tsanani da tsattsauran fahimta wasu sin fahimchi rayuwa wasu basu fahimta ba wasu suna iya ganin ra'ayin wasu suyi shiru wasu kuwa duk abin da suka gani wanda bai musu ba sai sunyi kacha kacha dashi angwaye da amare wadanda sukayi aure auren kirki auren soyayya auren rufin asiri suke jin dadin rayuwar aurensu muna muku fatan alkhairi Allah kuma ya kara muku dankon kauna ya karo farin ciki da soyayyar juna kuyi hakuri ku dinga kiyaye wasu abubuwan a wannan zamanin damuke a Facebook zaka iya yin hoto da wacce ba matarka ta halalinka ba ko kiyi hoto da mijin da ba naki na halalinki ba ki daura a media babu me cewa uffan amma ba dazarar kin ce zaki dora halal dinki anan zaki ga wasu kamar dama haushi suke sun tsani su ganku wanda zai fusata don ya ganku a hoto a gaske ma idan ya ganku zuciyarsa fusatar take muddin dai ba hoton da akayi anyi a yanayi ne da bai dace ba
👍 🙏 ❤️ 😢 🤣 19

Comments