Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 10, 2025 at 10:27 AM
Qanwata. Idan magana ta yi qarfi da ke da shi ta Aure, kun aminta da juna, kuma Iyaye sun karɓa, magana ta zauna. Duk lalurar da kike da ita ki sanar da shi (Banda ta zubar da mutunci). Shima ki san yanda za kiyi ya sanar da ke tashi, don ba'a AURE da rufa-rufa. Ko wani tabo ne Qato kike da shi, ki Labarta masa shi. Idan kinsan kina ciko da Qari ki sanar da shi "Wannan abin fa ba Nawa bane ba. Idan zai zo ku fahimci juna kizo masa a yanda kike sutura ba ta fitsara ba, amma dai kizo a yanda zai ga abin da xai AURA. Kamar Doguwar Riga da mayafinta, riga da zani da mayafi, da sauran sutura namu na gida da muka saba da su. In yaga zai dauka to zai tsaya yayi Hidimar daukan ki, idan ya ga bazai dauka ba to zai ajiye ki ya nemo wacce zai dauka😊 Amma shawara ce. Saboda sauqaqawa kai wasu matsalolin a gaba bayan Aure. Allah ya zaba Alkhairi. Ameeen. Zoohrah Oummu Deederht
👍 🙏 ❤️ 👏 😢 😮 🩲 28

Comments